Farfesa Wole Soyinka ya ce Shugaban Najeriya Muhammad Buhari har yanzu bai zama "cikakken farar hula ba, ta halayyarsa ga sauran al'ummar kasar."
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Jimeh Saleh, Editan sashen Hausa na BBC, yayin da ya kawo mana ziyara ofishinmu na Landan, kwanakin baya.
Ya ce shugaban ya gaza wajen shawo kan matsalar kiraye-kirayen raba kasar da kungiyar IPOB ke yi.
Farfesan ya ce har yanzu kasar tana amfani ne da kudin tsarin mulki wanda ya samu asali daga sojoji. "Kudin tsarin mulki ne da sojoji suka yi wa kansu," a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa: "Har yanzu sojoji suna rike da manyan mukamai a kasar ciki har da kujerar shugaban kasa."
"Fata muke su mayar da kansu fararen hula ciki da bai. Kuma wannan yana daya daga cikin gazawar Shugaba Buhari," in ji shi.
Shugaba Buhari ya taba zama shugaban mulkin sojin Najeriya a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985, kafin ya lashe zabe a shekarar 2015.
Har ila yau, farfesan ya ce shi bai ga dalilin da ya sa za a ci gaba da tsare jagoran 'yan Shia Sheikh Ibrahim Zakzaky ba, kuma "hakan kuskure ne."
Kimanin shekara biyu ke nan da gwamnatin kasar take tsare da malamin bayan rikicin mambobin kungiyarsa da sojojin kasar a Zariya.
Sai dai ya ce duk da cewa akwai fannoni da dama da gwamnatin Buhari "ta tafka kurakurai wadanda suka cancanci suka, akwai kuma fannonin da ya kamata a yaba mata".
Ya ba da misali da yadda gwamnati ta yi aiki wajen gano kudin da aka sace wadanda aka kai kasashen ketare.
Da kuma yadda aka sa "wadansu manyan jami'an gwamnati suka amayar da kudin da suka sace".
Hakazalika farfesan ya ce shugaban zai iya cewa ya cika aikin da aka zabe wato aikin yaki da cin hanci da rashawa da kuma shawon kan rikicin Boko Haram da kuma makamantanta.
Source: BBC Hausa
Title :
Haryanzu Sojane Ke Mulkin Nijeriya-Soyinka
Description : Farfesa Wole Soyinka ya ce Shugaban Najeriya Muhammad Buhari har yanzu bai zama "cikakken farar hula ba, ta halayyarsa ga sauran al...
Rating :
5