A can baya kadan mun bijiro da wani muhimmin al'amari, amma a mafi yawan lokuta ba a cika lura da shi ba a matsayin matsalar ma'aikata baki a kasar waje da suka dade: yadda zuwa kasar waje ta shafi mutumtaka, shi wani rukunin mutane da dawo wa gida.
Lamarin ya ja hankalin mafi yawan masu karatu wajen bayyana yadda suka kasance da al'amuran ban mamaki da suka hadu da su a lokacin da suka kewaya duniya.
Akwai tabbacin jin cewa kamar mutum bai taba zama a kasarsa ta haihuwa ba.
A gaskiya mafi yawan masu karatu sun kasance tamkar yadda marubucinmu ya shiga tsaka mai wuya, al'amarin da muke jin cewa mun yi iya kokarinmu wajen sajewa da al'umma da dawowarmu gida, bayan mun shafe tsawon lokaci a waje.
Babu inda ya kai gida?
A sharhin Faceboook, Wendy Skroch ya yi lamarin lakabin "kaduwar birkicewa al'ada.
"Akwai halin rashin matsuguni da ke tattare da mu a daukacin lamarin," kamar yadda ta rubuta.
"Jin cewa tamkar mutum bai taba zaman gida (kasar haihuwa) a ko'ina lamari ne da ke bayyane karara."
Mutane da dama kan kasance cikin damuwa tare da fafutikar sake kulla alaka lokacin da aka dawo gida.
Pete Jones, wanda ya bar Birtaniya a shekarar 2000 zuwa Denmark da Holland da Switzerland don zaman rayuwa, a rubuce ya ce: "Ba na jin dadin ziyarar Birtaniya a kwanaki kadan, har na ji akwai bukatar in fice daga kasar.
"Kawai na ji ba kasata ba ce! A gaskiya, ban san inda kasata take ba.
"Ban taba zaton haka zan ji a Switzerland ba, amma ina jin dadin rayuwa a nan," in ji shi. "A gaskiya, ban san inda kasata take ba."
Ka samu sauyi
A wajen wasu kuwa matakin da makusantansu ke dauka ke sanya wasu su dawo cikin kadaici da wahalar rayuwa.
"Dawowa Amurka bayan shafe shekara 26 a Austiraliya lamarin na haifar da kaduwa, kamar yadda yake kunshe a rubutun Bruce Felix.
"Kasancewa bako a inda ya kamata ya zama 'gida' na da matukar wahala a wasu lokutan.
Tasirantuwa da amfani da sababbin kalmomi ko furuce-furuce, amma ban da karin baki, kamar yadda ya yi nuni da cewa, isar da sako wajen mu'amala a kasarsa ta haihuwa na tattare da kalubale.
Bayan shafe shekara 20 a Amurka Mary Sue Connolly sai ta ji tamkar ana daukarta a matsayin bakuwa bayan komawarta Ireland.
"Na sauya shi ya sa nike jin ana daukata daban sanadiyyar hakan."
Rashin karya baki (kamar mutanen gida) mutane kawai za su tunanin ka zama daban."
"Sajewa (a cikin mutanenka) abu ne mai sauki, ta hanyar kin tattaunawa kan abin da ya gabata, domin akwai yiwuwar a dauka kawai ka yi bakam ne," a cewar sharhin Denis Gravel.
Allison Lee na iya ganewa. Ta koma Austiraliya bayan ta shafe shekara uku, bayan ga shekara shida da ta yi a Kudancin Amurka da Landan.
"Ana daukar tsawon lokacin kafin a kulla abota.. sannan babu wand ayake son jin labaranka."
Eunice Tsz Wa Ma, wanda dan asalin Hong Kong, har yanzu tana cike da kaduwar birkicewar al'ada ko da yake tana ziyartar birnin a ko wanne lokacin zafi.
"Ko wanne lokaci na koma sai kawai in ji tamkar an yasar (an bar ni a baya) da ni na wani lokaci, kamar ma a ce ni ne kadai ke tunani irin na da.
"Sannunku mutane! Kun tuna da ni?
Bayan ka dade ba ka nan, ta yaya za ka koma ka sake sajewa? Wasu daga cikin dabarun shawo kan lamarin da aka jarraba masu saukin aiwatarwa ne.
Ka guji koma irin aikin da ka bari a wuri guda da nau'in mutane guda idan za ka iya.
"Ka guji komawa irin aiki da ka yi a wrri guda da nau'in mutane guda idan za ka iya," kamar yadda mazaunin Birtaniya John Simpson ya bayar da shawara.
"Za a hadu wajen adawa, inda al'amuran da ake takaddama akai ba su da muhimmanci."
Vesna Thomas, wadda aka dawo da ita zuwa Sydney bayan ta shafe shekara 16 a Amurka da Singapore, ta kasa yin abota/kawance da mutane bayan da shekarunta suka kai 40 da doriya.
Kwatsam sai ta kafa kungiyar masu karatun litattafai, ta rika aikin wucin gadi a wajen, tare da aikin sa-kai na koyarwa a makaranta.
"Abin ban dariyar shi ne, daukacin wadanda suka shiga kungiyata ta makarantan littafai bakin ma'aikata ne 'yan kasar waje.
"Tun da ka kan ja hankalin wasu da zarar sun fahimci irin abin da kake ji (ko yanayin da kake ciki).
A gaskiya, wasu daga wadanda ke kokarin komawa wani gari sukan tafi kai tsaye don neman inda za su hadu da al'ummomin bakin ma'aikata 'yan kasar waje.
"Wannan na matukar taimakawa saboda na yi kokarin kin gwamuwa da dumbin Amurkawa lokacin da nake kasar waje, kuma sai na rika jin karakainar al'adun Amurkawa da ganinsu, inda na dan samu saukin sajewa, kamar yadda Alexis Gordon ya bayyana a rubutunsa.
A wajen wasu kuwa komawa gida, tamkar ko wanne irin tura mutum wani wuri mai nisa ne.
"Na yanke cewa zan dauki dawowar da ni tamkar wani aikin bakon da aka tura kasar waje, ko da yake a gaskiya wuri ne da na saba da shi, nasan (na iya) harshensu," a cewar Katrina Gonnnerman.
"Wannan ya taimaka mini na daidaita zama."
"Na shafe tsawon shekara 30 ba na nan (kuma) duk sa'adda na dawo Amurka na kan yi abin da zan yi tamkar ina wata kasar waje, (sannan) ina cike da mamaki wajen samun sauki aiwatar da al'amura a ko wacce rana," a cewar Mark Sebastian Orr.
Ta ya ya za ka sake sajewa? Ba ka sani ba!
Ta yiwu mafi ban mamaki amsar da za ka ba mu kan dabarun sake sajewa wani babban kalubale ne da tambayar da ta bijirro da shi a kashin kanta.
Mafi yawan masu karatu na ganin sake gyara zama a kasar da aka ce ta haihuwarka ce na da wuya, sai dai kacokam ba lamari da ya zama dole ba.
Nicole Jones ya mallaki fasfo uku, kuma ya zauna a kasashe biyar. "Ban taba tunanin fifikon kyawun wani wuri ba, don kyakkyawan abu da muna a bayyane suke karara.
"Ina jin cewa ni mazaunin duniya, kuma ina alfahari da haka. Kokarin dawowa kasashe inda ka bari a da kuskure ne.
"Ba za ka iya ba (sake sajewa)," a cewar sharhin Paula Alvarez Couceiro.
"Ka fahimci cewa kasancewa ka zauna a al'ummomi masu mabambanta al'adu da dama, kimar mutumtakarka da tunaninka sun sauya, kuma kokarin ka dawo ka saje da abin da ka bari a da kuskure ne da zai kawo tarnaki ga ci gaban da ka samu."
Wadannan bayanai na fada mana cewa a wajen dimbin ma'aikata baki 'yan kasar waje sake tunanin sajewa a kasar haihiuwarsu da siffantuwa da al'adunsu ba aiki ba ne na kai-tsaye yayin da suka dawo "kasar da suka fice daga ciki."
Ta yiwu a samu kwanciyar hankali a tattare da mazaunan duniya, wadanda sake sajewa zabi ne, amma ba tilas ba ne.
Source: BBC Hausa