Wata girgizar kasa mai karfin sama da maki bakwai ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 a yankin kan iyaka na arewaci tsakanin Iran da Iraki.
Akalla mutum 129 ne suka mutu a lardin Kermanshah na kasar Iran a cewar jami'ai ta kafar talbijin din kasar.
Haka zalika, girgizar ta haddasa mutuwar wasu mutane a makwabciyar kasar wato Iraki baya ga jikkata wasu dumbin mutanen a Iran.
An samu katsewar hasken lantarki da ruwan sha, baya ga yankewar hanyoyi a cikin birane da kauyukan da iftila'in ya shafa.
Yankewar hanyoyi sakamakon girgizar kasar kuma na kawo cikas ga ayyukan ceto.
Tsagewar da kasa ta yi ya kai har kusa da kan iyakar Iraki kusa da birnin Kurdawa na Halabja.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum shida sakamakon girgizar kasar a Iraki.
Haka kuma, kasashe kamarsu Israila da Kuwaiti duk sun ji rugugin wannan girgizar kasa.
Source: BBC Hausa
Title :
Girgizan Kasa Ya Hallaka Sama Da Mutum Dari A Iran
Description : Wata girgizar kasa mai karfin sama da maki bakwai ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100 a yankin kan iyaka na arewaci tsakanin Iran da Ira...
Rating :
5