Tsohon dan kwallon Manchester United, Ryan Giggs ya karbi aikin tuntuba a matsayin daraktan makarantar koyon tamaula ta Vietnam.
Giggs mai shekara 43, zai yi aiki a cibiyar tara kudi don zakulo matasan tamaula masu fasaha ta Vietname, domin horar da 'yan wasa da kuma koci-koci.
Tsohon dan wasan tawagar Wales, ya amince da yarjejeniyar shekara biyu, inda zai dinda zuwa Vietnam sau biyu a shekara domin gabatar da aikinsa.
Rabon da Giggs a dama da shi a fagen kwallon kafa tun bayan da Manchester United ta sallami Luis van Gaal a watan Mayun 2016.
A mako mai zuwa Giggs zai ziyarci Vietnam domin bikin kaddamar da shi, inda Paul Scholes ne zai zama babban bako a bikin.
Source: BBC Hausa
Title :
Giggs Zaiyi Daraktan Makarantar Kwallo
Description : Tsohon dan kwallon Manchester United, Ryan Giggs ya karbi aikin tuntuba a matsayin daraktan makarantar koyon tamaula ta Vietnam. Giggs mai ...
Rating :
5