Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta ce dole ne hukumar wasanni ta kasar Gambia, ta soke hukuncinta na dakatar da shugabancin hukumar kwallon kafa ta kasar nan da ranar Litinin 27 ga watan nan na Nuwamba.
A wasikar da Fifa ta aika wa hukumar ta yi gargadin cewa idan har ba a yi hakan ba zuwa wa'adin, ta ce za ta dauki mataki wanda zai iya hadawa da hana shigar kasar ta gambia harkokin wasannin kwalllon kafa na duniya.
Har zuwa yanzu dai hukumar wasannin ta Gambia ba ta ce komai ba game da wa'adin na hukumar kwallon kafar ta duniya.
TALLA
A ranar 10 ga watan nan na Nuwamba ne hukumar wasannin ta kasar ta dakatar da shugabancin hukumar kwallon kafar ta Gambia a kan zargin aikata almundahana.
Hukumar ta ce ta dakatar da shugabannin ne domin a samu damar gudanar da bincike kan zargin ba tare da sun yi katsalandan a ciki ba.
Idan dai har Fifa ta dakatar da kasar, to hakan zai hana kungiyoyinta shiga wasannin nahiyar Afirka, kuma ba wata tawagar wasan kasar da za ta shiga wata gasa da Fifa ta amince da ita.
Haka kuma hukuncin zai iya hana zuwan alkalin wasa Papa Gassama, wanda shi ne ke samun lambar gwarzon lafiri na Afirka karo uku, gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi a Rasha.
Source: BBC Hausa
Title :
Fifa Zata Dakatar Da Gasar Gambia
Description : Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta ce dole ne hukumar wasanni ta kasar Gambia, ta soke hukuncinta na dakatar da shugabancin hukumar kwa...
Rating :
5