Borussia Dortmund ta tabbatar da cewa ta dawo da dan wasanta na gaba na kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang bayan dakatar da shi da ta yi kwanan nan, domin hukunta shi kan rashin da'a.
A yanzu kenan zai yi wa kungiyar ta Jamus wasa a karawar da za ta yi a gidanta gobe Talata da Tottenham a gasar cin kofin Zakarun Turai.
Dan wasan bai taka wa Dortmund leda ba a karawar da Stuttgart ta doke su 2-1 a gasar Jamus ta Bundesliga, ranar Juma'a a matsayin horon da aka yi masa na zuwa filin atisaye latti, da kuma hoton bidiyon da ya dauka a lokacin atisaye, wanda bai yi shi da izini ba.
Kungiyar za ta zaku ta ga dan wasan wanda ya ci kwallo 15 a wasa 12 na farko a kakar nan, ya dawo kan ganiyarsa ta daga raga, wanda rabonsa da haka tun ranar 14 ga watan Oktoba.
Dortmund na matsayi na uku ne a rukuninsu na takwas (Group H), a gasar ta Zakarun Turai, wanda hakan ya sa dole sai ta doke Tottenham ta daya, wadda tuni ta tsallake zuwa mataki na gaba, kuma ta yi fatan Real Madrid ta kasa yin nasara a karawarta da APOEL ta Cyprus a ranar Talatar (gobe), domin ta ci gaba da kasancewa da 'yar damarta ta kaiwa zagayen 'yan 16.
Wasannin Zakarun Turai na ranar Talata;
Spartak Moskva da Maribor
Beşiktaş da Porto
Sevilla da Liverpool
Manchester City da Feyenoord
Napoli da Shakhtar Donetsk
Monaco da RB Leipzig
APOEL da Real Madrid
Borussia Dortmund da Tottenham Hotspur
A ranar Laraba ne kuma za a yi sauran wasannin gasar guda takwas kamar haka;
CSKA Moskva da Benfica
Qarabağ da Chelsea
Basel da Manchester United
Anderlecht da Bayern München
PSG da Celtic
Atlético Madrid da Roma
Juventus da Barcelona da Olympiakos Piraeus
Source: BBC Hausa
Title :
Dortmund Zata Dawo Da Aubameyang A Kofin Zakarun Turai
Description : Borussia Dortmund ta tabbatar da cewa ta dawo da dan wasanta na gaba na kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang bayan dakatar da shi da ta yi ...
Rating :
5