Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang a matakin da ta dauka na ladabtar da shi.
Dan wasan tawagar kwallon kafar Gabon ba zai buga wa Dortmund wasan Bundesliga da za ta fafata da VFB Stuttgart a ranar Juma'a ba.
Dortmund ta sanar da dakatar da dan kwallon mai shekara 28 bisa mayar wa da wani magoyin baya martani da ya yi tambaya a shafin sada zumunta na Twitter, amma kungiyar ba ta fayyace komai ba.
A bara ma sai da Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang, bayan da ya je Italiya ba tare da sanin kungiyar ba.
Wasa ya fara juya wa Dortmund baya, inda ta yi rashin nasara a fafatawa uku daga hudu da ta yi kwanan nan a Bundesliga ta kuma koma ta uku a kan teburin gasar bana.
Source: BBC Hausa
Title :
Dortmund Ta Dakatar Da Aubameyang
Description : Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta dakatar da Pierre-Emerick Aubameyang a matakin da ta dauka na ladabtar da shi. Dan wasan tawa...
Rating :
5