A Najeriya, yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da dokar hana kiwo da ta soma aiki a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar kasar, ministan noma da raya karkara na kasar Audu Ogbeh, ya shaida wa BBC cewa saboda rikicin da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya, dole ne a kintsa makiyayan wuri guda, sannan za'a samar da wurare na musamman domin shanu inda za'a basu ciyawa da ruwa mai kyau.
Ministan ya ce, idan har aka yi hakan, to su kansu makiyayan ba za su so su yi yawo ba, kuma ko ba komai an kare su daga barazanar masu satar shanu.
Dangane da batun kafa dokar hana kiwo a jihar Benue, ministan ya ce matsin lambar mutane ne ya tilasta wa gwamnan jihar kafa wannan doka saboda tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin manoma da makiyaya a jihar.
Mr Audu Ogbeh, ya ce nan ba da jimawa ba za'a fara aiki a wuraren kiwo na musamman da aka kebe, na farko a jihar Kano, sai kuma na jihar Neja.
Ya ce da sannu a hankali mutane za su fahimci cewa lallai ana bukatar naman shanu, don haka dole a inganta yadda ake kiwon shanun.
Ministan ya ce, idan aka kori makiyaya to a ina za'a samu naman da za a ci? don haka dole ne a tanadi kebabbun wuraren kiwo na musamman, kuma za'a yi hakan ne ta hada hannu da gwamnatocin jihohin kasar
Source: BBC Hausa
Title :
Dole A Samar Da Wuraren Kiwo Na Musamman A Kasar Nan
Description : A Najeriya, yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da dokar hana kiwo da ta soma aiki a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar kasar, ministan ...
Rating :
5