Chelsea ta casa West Bromwich Albion 4-0 a wasan mako na 12 a gasar Premier da suka kara a ranar Asabar.
Morata ne ya fara ci wa Chelsea kwallo, sai Eden Hazard da ya ci na biyu, sannan Alonso ya ci ta uku kafin a je hutun rabin lokaci.
Bayan da aka dawo ne daga hutu Eden Hazard ya ci ta hudu kuma ta biyu a karawar.
Chelsea ta hada maki 25 a wasa 12 da ta buga a gasar, ita kuwa West Brom tana nan da makinta 10.
Chelsea za ta ziyarci Liverpool a wasan mako na 13 a gasar ta Premier, ita kuwa West Brom za ta fafata da Tottenham a Wembley.
Source: BBC Hausa
Title :
Chelsea Ta Lallasa Westbrom Cikin Ruwan Sanyi
Description : Chelsea ta casa West Bromwich Albion 4-0 a wasan mako na 12 a gasar Premier da suka kara a ranar Asabar. Morata ne ya fara ci wa Chelsea kw...
Rating :
5