Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana shirin kashe kimanin naira biliyan daya a badi wajen tafiye-tafiye, kamar yadda daftarin kasafin kudin kasar wanda ofishin kula da kasafin kudi ya bayyana.
Kamar yadda ofishin ya ce shugaban zai kashe naira miliyan 751.3 wajen tafiye-tafiyen kasashen ketare, yayin da zai kashe naira miliyan 250.02 wajen tafiye-tafiyen cikin gida.
Haka zalika daftarin kasafin kudin ya bayyana cewa za a kashe naira miliyan 907 wajen sayen sabbin motoci da kuma sayo kayayyakin gyaransu a shekarar 2018.
Har ila yau za a sayi tayoyin motoci masu silke a kan naira miliyan 83.77 da sauran motoci da motocin daukar marasa lafiya da sauransu.
Mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo zai kashe jimullar naira miliyan 301.04 a kan tafiye-tafiye.
A makon jiya ne Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.6 ga majalisar dokokin kasar.
A jawabinsa ga majalisar dokin kasar yayin gabatar da kasafin, ya ce gwamantinsa tana tsammanin za ta samu kimanin naira tiriliyan 2.442 daga albarkatun mai.
Ya kara da cewa Najeriya tana hasashen cewa za ta sayar da gangar mai sama da miliyan biyu a ko wacce rana.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Zai Kashe Miliyan Dubu A Tafiye-Tafiye A 2018
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana shirin kashe kimanin naira biliyan daya a badi wajen tafiye-tafiye, kamar yadda daftarin kasafin kud...
Rating :
5