Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan murnar cika shekara 60 a duniya.
A ranar Litinin ne Mista Jonathan zai cika shekara 60 da haihuwa.
Shugaba Buhari ya yaba wa tsohon shugaban inda yake cewa: "ya fara rike mukamin mataimakin gwamna ne, kafin daga bisani ya zama gwamna, kafin ya zama shugaban kasa na tsawon shekara shida, ya fara zama mataimakin shugaban kasa ne".
Daga nan shugaban ya ce yana taya jam'iyya adawa ta PDP da 'yan uwa da abokan arzikin Mista Jonathan murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kamar yadda ya ce a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mista Femi Adenisa ya aike wa BBC.
A watan Maris din shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya lashe babban zaben kasar, bayan samun nasara a kan babban abokin hamayyasa Mista Goodluck Jonathan wanda ke kan karagar mulki a lokacin.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Taya Jonathan Murnan Cika Shekaru 60
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan murnar cika shekara 60 a duniya. A ranar Litinin ne Mist...
Rating :
5