A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa jihar Ebonyi a ziyararsa ta farko da ya kai yankin Kudu maso Gabashin kasar tun bayan darewarsa kan mulki.
Gwamnonin Ebonyi da Abia da Enugu da dumbin jami'an tsaro da kuma sarakunan gargajiya ne suka hallara a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke birnin Abakaliki inda suka tarbi shugaban kasar.
A ziyarar da shugaban zai yi ta kwanaki biyu zai kuma ziyarci jihar Anambar baya ga jihar Ebonyi da ya fara sauka.
Tuni dai wasu al'ummar Igbo a yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun yi maraba ga ziyarar da shugaban kasar zai kai jihohinsu daga ranar Talata.
Akasarin mutanen da BBC ta zanta da su ta wayar tarho sun ce suna wa Shugaba Muhammadu Buhari maraba a wannan ziyara ta farko da zai kai yankin.
Wasu Igbo dai sun sha sukar Muhammadu Buhari kan yadda suka ce ba ya damawa da al'ummar yankin a gwamnatinsa.
Al'amarin da ya zafafa rajin ballewa daga Najeriya a tsakanin wasu matasan yanki a baya-bayan nan.
Sai dai, wani Igbo ya ce: "Za mu yi masa marhabin ta yadda zai yi wa yankinsu wani aikin ci gaban kasa. Ai Najeriya kasarmu ce."
Za mu yi murna da zuwansa, in ji shi.
Ita ma wata ta ce "Ai babu damuwa! Ina farin ciki da haka. Ziyarar za ta sa mu ji cewa Najeriya daya ce babu batun nuna bambanci tsakanin Bahaushe ko Bayarabe ko Igbo."
Ta ce wato dukkan al'ummar kasar daya suke. "Ina kaunar wannan ziyara da Buhari da zai kawo yankinmu".
Haka zalika, mutanen yankin na Kudu Maso Gabas na zargin gwamnatin Buhari da rashin gudanar da ayyukan raya kasa, inda suka ce yana nuna fifiko a mulkinsa.
Shi kuma wani tsohon dan jarida a yankin, Kalu Ezee na cewa da ma ya kamata Buhari ya kai wannan ziyara.
A cewarsa tun da aka kammala zabe, Buhari bai samu damar ziyartar yankin ba, don haka zuwansa zai magance wasu abubuwa da dama.
"Ka san mutanenmu kafin ya zo, suna gani kamar bai yi musu wasu ayyukan alheri sosai ba, don haka wannan dama ce gare shi ya fada musu abubuwan da ke zuciyarsa," in ji Mista Kalu.
Ya ce mutanen yankin su ma za su samu damar yi masa bayani game da matsalolin da suke ci wa al'ummar yankin tuwo a kwarya.
A cewarsa: "Za su yi masa magana a kan (mawuyacin hali da) hanyoyin gwamnatin tarayya da ke yanki. Za su yi magana a kan (aikin) gadar Neja ta biyu, wato gadar nan ta Onacha, ka san ta dade ana maganarta."
Dan jaridar ya ce al'ummar yankin za su so su bijirowa da Shugaba Buhari batun samar da ayyukan yi ga matasa da kuma tsaro.
"Za su yi magana game da rikicin nan da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya, Mista Kalu ya ce.
An tambaye shi ko za a bijiro wa shugaban maganar kafa kasar Biafra sai ya ce: "Maganar Biafra ba za ta taso ba, don kuwa kungiyar Ohaneze Ndigbo ta rika ta magance al'amarin".
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Ya Isa Jihar Ebonyi
Description : A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa jihar Ebonyi a ziyararsa ta farko da ya kai yankin Kudu maso Gabashin kasar tu...
Rating :
5