Masharhanta harkokin siyasar Najeriya na bayyana albarkacin bakunansu kan ziyarar da Shugaba Buhari a yankin Kudu Maso Gabashin kasar, wadda suka ce tun tuni ya kamata a ce ya je.
Dr. Abubakar Kari ya ce "ina ga saboda mai yiwuwa sha'awar da yake da ita ta tsayawa takara a gaba, da alama zai rika amfani da duk damar da ta zo masa."
Ya ce tuni shugaban ma ya fara amfani da irin wadannan damammakin, bayan dakushe kaifin masu rajin kafa Biafra.
Zuwa yanzu dai shugaban bai fito ya furta da bakinsa cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019 ba.
Ko da yake, kiraye-kirayen Buhari ya yi tazarcen a fadin kasar suna ci gaba da karuwa.
Shugaba Buhari ya fara ziyarar wuni biyu a jihohin Ebonyi da Anambra, karon farko bayan hawansa kan karagar mulkin kasar a 2015.
Wasu al'ummar yankin Igbo sun rika sukar shugaban kasar tare da zargin cewa gwamnatinsa ba ta damawa da su, sannan kuma tana nuna fifiko.
Dr. Kari ya ce bayan lafawar guguwar kafa Biafra da ta yi zafi a kwanan baya, sai shugaban "ya zagaya ta baya ya dinga zawarcin manya-manyansu."
A cewarsa ko nuna damuwar da Shugaba Buhari ya yi game da rashin lafiyar tsohon shugaban kasa Alex Ekweme da kuma sakwannin taya murna da ya rika aika ga manyan al'ummar Igbo.
"Da kuma a duk lokacin da ya yi kalami zai nuna cewa gwamnatinna tana nan ta yi shiri don sake gina gadar nan ta Onaca, sannan kuma ya yi maganar cewa za a yi sabon asibiti a Umuahia.
Za a gyara musu hanyoyi manya-manya, to duka wadannan zawarci ne, in ji Dr. Kari"
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Na Zawarcin Sake Tsayawa Takara-Dr Kari
Description : Masharhanta harkokin siyasar Najeriya na bayyana albarkacin bakunansu kan ziyarar da Shugaba Buhari a yankin Kudu Maso Gabashin kasar, wadda...
Rating :
5