Wani masani kan sha'anin tsaro a Najeriya, ya yi ikirarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya amince 'yan sandan kasar na da gazawa ta fuskar horo da kuma binciken masu laifi.
"Kasawa ta fuskar tattara shaidu wurin kama wadanda ake zargi, wanda kuma shi ne ke hana hukunta masu laifi a kasar," in ji masanin harkokin tsaron.
Ya ce a kan haka ne Muhammadu Buhari ya yi alkawari a jawabinsa na hawa kan mulki don kawo sauyi a rundunar 'yan sanda don karfafa mata gwiwar yaki da laifuka.
"Sai dai har yanzu ba mu ga canji ba ga wannan al'amari."
Da yake karin haske kan wani rahoto da wata kungiya mai bincike kan harkokin aikin 'yan sanda a duniya ta fitar a baya-bayan nan inda ta sanya 'yan sandan Najeriya a matsayin kurar baya ta fuskar iya aiki.
Malam Kabiru Adamu ya ce bai yi mamaki ba.
Kungiyar nazari da binciken kimiyyar ayyukan 'yan sanda da hadin gwiwar wata cibiya ne suka fitar da rahoton, bayan tattaunawa da kwararru.
A mizanin kungiyar, kamata ya yi a samu dan sanda 300 da ke kula da adadin 'yan kasa 100,000 sai dai a Najeriya dan sanda 219 ne ke kare duk mutum 100,000, "hakan kuma ya gaza," in ji masanin.
A cewarsa batun karbuwar aikin 'yan sandan ma a idon 'yan kasa, al'amari ne da masanin ya ce nan akwai gibi a Najeriya.
Kabiru Adamu ya ce "batun tsarin gudanar da aikin 'yan sanda ma a Najeriya, akwai kasawa cikinsa."
Ya ce abin da ya fitowa fili ma a yanzu shi ne yadda dakarun sojin kasar ke gudanar da ayyukan da suka kamata a ce 'yan sandan ne suke yi a cikin jihohi guda 28 cikin 36 na kasar.
Binciken dai kan kwazon aikin 'yan sanda da sauran jami'an tsaron cikin gida a duniya ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da sukar rundunar 'yan sandan Najeriya kan rashin iya aiki da cin hanci da rashawa.
Ko da yake, a kullum 'yan sandan Najeriya sukan musanta irin wadannan zarge-zarge.
Masanin ya ce ko da yake, akwai dan ci gaba amma har yanzu akwai sauran rina a kaba game da ci gaban aikin 'yan sanda a Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Kansa Yasan Da Gazawar 'Yan Sanda-Masani
Description : Wani masani kan sha'anin tsaro a Najeriya, ya yi ikirarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari da kansa ya amince 'yan sandan kasar na da g...
Rating :
5