Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafa ta Italiya, Gianluigi Buffon, yana zubar da hawaye ya nemi gafarar magoya bayan kasar, bayan da suka kasa samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Kyaftin din ya yi ritaya daga buga wa Italiya tamaula, bayan da kasar ta kasa yin nasara a kan Sweden a wasannin da suka buga gida da waje don neman tikitin shiga gasar ta duniya.
Italiya ta tashi wasa babu ci da Sweden a gida, bayan da a wasan farko ta sha kashi da 1-0, hakan ne ya sa a karo na farko tun 1958 ba za a ga kasar a gasar ba.
TALLA
Buffon mai shekara 39 ya ce, ''Abin kunya ne a lokacin wasana na karshe da na buga wa Italiya na ci karo da kasa zuwa gasar cin kofin duniya''.
Shi ma Andrea Barzagli mai taka-leda a Juventus, da dan wasan Roma, Daniele de Rossi, sun yi ritaya, ana kuma sa ran Giorgio Chiellini zai bi sahunsu; 'yan wasan uku a tsakaninsu sun yi wa Italiya wasa 461.
Buffon mai tsaron ragar Juventus ya buga wa Italiya wasanni 175 a shekara 20 da ya yi a tawagar, ya kuma lashe kofin duniya a 2006.
Source: BBC Hausa
Title :
Buffon Yayi Ritaya Bayan Italiya Tasha Kunya
Description : Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafa ta Italiya, Gianluigi Buffon, yana zubar da hawaye ya nemi gafarar magoya bayan kasar, bayan da suka k...
Rating :
5