GAn yi wa tsohon kwamandan Sabiyawan Bosniya Ratko Mladic daurin rai da rai kan laifin kisan kiyashi da kuma sauran laifukan cin zarafin bil'adama a yakin Bosniya na shekarun 1990.
An yi wa mutumin lakabi da sunan "mai yi wa mutanen Bosniya kisan gilla".
Mladic ya jagoranci dakaru a lokacin da aka yi wa Musulman Bosniya kisan kiyashi a garin Srebrenica da kuma kawanyar da aka yi wa birnin Sarajevo.
Kotun Majalisar Dinkin Duniya a Hague ta same shi da laifi a tuhumu-tuhume 10 cikin 11.
Mladic, mai shekara 74, bai kasance a kotu ba a lokacin da aka karanta hukuncin.
An fitar da shi daga kotun sabo da ya yi wa alkalan kotun ihu.
Alkalan sun yi watsi da damar da masu kare shi suka nema na a dakatar da zaman kotun saboda hawan jinin Mladic.
A lokacin da aka fara zaman kotun ya nuna alamar kasancewa cikin annashuwa inda ya yi ta murmushi.
Mladic ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka yi mishi, kuma luyansa ya ce zai daukaka kara.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyiwa Mladic Daurin Rai da Rai Kan Kashe Musulman Bosnia
Description : GAn yi wa tsohon kwamandan Sabiyawan Bosniya Ratko Mladic daurin rai da rai kan laifin kisan kiyashi da kuma sauran laifukan cin zarafin bil...
Rating :
5