Manchester United ta kuskure damarta ta tsallakawa zagaye na gaba na kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai bayan da ta yi sake FC Basel ta zura mata kwallo daya a minti na 89 a Switzerland.
United ce ta kankane wasan a kashin farko inda Marouane Fellaini da Marcos Rojo suka kai hare-haren da kiris su ci amma bal din ta doki turken raga.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma sai labari ya sauya, 'yan Basel suka farfado suka rika kai farmaki a kai a kai.
Ana dab da tashi ne a minti na 89 Micheal Lang ya daga ragar United da kwallon da Raoul Petretta ya kwararo ta gefen hagu.
A daya karawar da aka yi ta rukunin nasu Spartak Moscow a gidanta ta doke Benfica 2-0.
Idan Manchester United ta samu maki ko da daya a karawar da za ta yi ta gaba kuma ta karshe da Spartak Moscow, ranar biyar ga watan Disamba, hakan zai ba ta damar tsallakawa zuwa matakin na sili-daya-kwale.
A yanzu Man United ta ci gaba da zama ta daya a rukuninsu na daya (Group A) da maki 12, sai Basel mai maki tara, yayin da Spartak Moscow take ta uku ita ma da maki tara amma da bashin kwallo daya, Benfica kuma tana ta karshe ba maki ko daya.
Source: BBC Hausa
Title :
Basel Tadoke Man United Daci Daya Mai Ban Haushi
Description : Manchester United ta kuskure damarta ta tsallakawa zagaye na gaba na kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai bayan da ta yi sake FC Basel ta zur...
Rating :
5