A karon farko Arsenal ta ci Tottenham 2-0 a fafatawa bakwai da suka buga a gasar Premier a wasan mako na 12 da suka kara a ranar Asabar.
Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun Shkodran Mustafi sannan Alexis Sanchez ya kara ta biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci.
Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki 22 a wasa 12 da ta buga a gasar, ita kuwa Tottenham tana nan da makinta 23.
Arsenal ta yi wasa 17 a Emirates ba a doke ta ba, tun bayan da Bayern Munich ta yi nasara a kanta da ci 5-1 a watan Maris, jumulla ta ci wasa 15 ta yi canjaras a karawa biyu.
Gunners za ta buga wasan mako na 13 da Burnley, ita kuwa Tottenham za ta karbi bakuncin West Brom.
Source: BBC Hausa
Title :
Arsenal Ta Dau Maki Uku Akan Tottenham
Description : A karon farko Arsenal ta ci Tottenham 2-0 a fafatawa bakwai da suka buga a gasar Premier a wasan mako na 12 da suka kara a ranar Asabar. Ar...
Rating :
5