Sojojin Zimbabwe sun yi wa Shugaba Robert Mugabe daurin talala a babban birnin kasar Harare, in ji shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma.
Mista Mugabe ya shaida wa Mista Zuma ta wayar tarho cewa yana cikin koshin lafiya, in ji ofishin shugaban Afirka ta Kudun.
Sojoji sun ta yin sintiri a babban birnin kasar, Harare, bayan sun karbe iko da gidan talabijin din kasar kuma sun ce suna hakon masu laifi ne.
Wannan yunkurin ka iya kasancewa kokarin maye gurbin Mista Mugabe da mataimakinsa da aka kora, Emmerson Mnangagwa, in ji wakiliyar BBC.
Yadda sojoji suka kwace iko a Zimbabwe
Korar Mista Mnangagwa a makon da ya wuce ya sa ana ganin matar Mista Mugabe, Grace, ce za ta gaje shi a mulki.
Mista Mugabe, mai shekara 93, ya mamaye fagen siyasar kasar tun da ta sami 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1980.
Bayan an shafe kwanaki ana zaman dar-dar da kuma yada jita-jita, sojoji sun karbe iko da kafar watsa labarai mallakar Zimbabwe, ZBC cikin daren ranar Talata.
Wani jami'in sojin Zimbabwean, Manjo Janar General Sibusiso Moyo, ya yi wani jawabi a gidan talabijin mallakar kasar cewa babu wani juyin mulki a kasar, amma ya ce sojojin suna hakon masu laifi ne da ke kewaye da Shugaba Mugabe.
Jaridar Chronicle wadda ke karkashin ikon gwamnatin Zimbabwe a birnin Bulawayo, ta wallafa labarai na musamman game da rikicin kasar.
Ta fito da kanun da ke cewa: "Sojoji sun karbe iko", tana mai cewa sojoji sun karbe mulki domin su "kakkabe masu laifuka na jam'iyyar ZANU-PF".
Me ya sa sojoji ba sa son amfani da kalmar juyin mulki?
Rashin ambatar kalmar juyin mulki shi ne abun da ya fito cikin jawabin da manjo janar Sibusiso Moyo ya gabatar a kafar yada labaran Zimbabwe ZBC, da safiyar Laraba.
Janar Moyo ya jaddada cewa wannan ba juyin mulki ba ne.
Saboda haka me ya sa wannan yake da muhimmanci?
Kungiyar Tarayyar Afirka AU, da kuma kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (Sadc), ba su lamunci juyin mulki ba.
An ga hakan ya faru a Burkina Faso a shekarar 2015 a lokacin da kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Burkina Faso ta kuma kakaba takunkumi kan wadanda suka yi yunkurin juyin mulki, shekara daya bayan an tumbuke Blaise Compaore wanda ya dade yana mulkar kasar.
Ba abun mamaki ba ne cewa rundunar sojin kasar tana ta kokarin nuna cewa farar hula ce take iko da kasar har yanzu.
Tuni dai, Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya fitar da wata sanarwa a madadin SADC cewa yankin ba zai lamunci juyin mulki
'Sojoji na dukan 'yan sanda'
Wata mata da ke zaune a Harare, Denissa Moyannah, ta shaida wa BBC cewa ta kai ziyara tsakiyar birnin, daga gidanta da ke unguwar masu hannu da shuni ta Borrowdale da safiyar Laraba.
Ta ce motoci masu sulke sun cika ko ina a tsakiyar birnin inda suke tsayar da ababen hawa a tsakiyar hanya.
Ta ce sojoji na dukan 'yan sanda, sannan kuma kafar talabijin din kasar tana saka wakokin neman 'yanci.
Miss Moyannah ta kuma ce kura ta lafa a babban birnin Zimbabwe din.
Source:BBC Hausa
Title :
Anyi Wa Shugaba Mugabe Daurin Talala Zimbabwe
Description : Sojojin Zimbabwe sun yi wa Shugaba Robert Mugabe daurin talala a babban birnin kasar Harare, in ji shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma. Mist...
Rating :
5