Masu zanga-zanga sun nufi fadar Shugaban Zimbabwe Shugaba Robert Mugabe don su bayyana bukatarsu ta shugaban ya sauka daga mulki.
Gangamin ya samu goyon bayan rundunar sojin kasar wadda ta kifar da gwamnatin kasar a ranar Laraba.
Wakilin BBC ya ce mutane suna jinjinawa sojojin kasar yayin gangamin.
Wani bangare na jam'iyya mai mulki ta Zanu-PF da kuma wadansu tsofaffin sojin kasar wadanda da a baya suke goyon bayan shugaban kasar, yanzu sun ce lokaci ya yi da zai yi murabus.
Shugaban kungiyar tsofaffin sojojin kasar, Christopher Mutsvangwa, ya bukaci al'ummar kasar da su fito zanga-zangar adawa da mulkin Shugaba Mugabe.
Sojojin Zimbabwe sun yi wa Mista Mugabe daurin talala a birnin kasar Harare ranar Laraba.
A ranar Juma'a ne aka ga Shugaba Mugabe na tafiya kan jar darduma sanye da kayan bikin kammala karatun digiri, inda ya shiga cikin taron daliban jami'a da ke bikin kammala karatu suna kuma rera taken kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyi Gangamin Adawa Da Mugabe A Zimbabwe
Description : Masu zanga-zanga sun nufi fadar Shugaban Zimbabwe Shugaba Robert Mugabe don su bayyana bukatarsu ta shugaban ya sauka daga mulki. Gangamin ...
Rating :
5