An soki wani ministan jam'iyya mai mulki a kasar Indiya a kan yin fitsari a titi, duk da kokari da gwamnati take yi wajen jayo hankalin mutane su rika yin amfani da bandakuna.
A ranar bandaki ta duniya ne aka nuna bidiyon Ram Shinde na yin fitsari a titi, inda aka yada bidiyon sama da sau dubu a shafukan sada zumunta.
Masu adawa sun ce hakan ya nuna cewa gangamin da Firaiminista Narendra Modi ya yi a kan tsafta bai yi amfani ba
Sai dai ministan ya ce ya yi haka ne saboda a matse yake, kuma bai samu bandaki a kusa ba.
Wani minista daga jam'iyyar Mista Modi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na PTI cewa: "Tafiyar da na ci gaba da yi ne cikin tsanannin zafi da kura ta haddasa min rashin lafiya. Kuma ina fama da zazzabi."
"Ta yaya firaiminista zai yi tsammanin mutane su bi doka bayan ministocinsa na karya wa?"
A shekarar 2014 ne Mista Modi ya kaddamar da wani gangami na tsaftace kasar don kara tabbatar da tsafta.
Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta gina miliyoyin bandakuna a fadin kasar.
Sai dai masu suka sun ce shirin bai samu tagomashi na a zo a ga ni ba a yawancin yankunan Indiya.
A wani rahoto da kungiyar agaji ta WaterAid ta fitar a kan ranar bandaki ta duniya da aka yi ranar Lahadi ya ce, har yanzu fiye da mutum miliyan 700 na kasar Indiya na fama da matsalar yin fitsari a titi, ko kuma yin amfani da bandakuna marasa kyau.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyi Allah Wadai Da Ministan Da Yayi Fitsari Akan Titi
Description : An soki wani ministan jam'iyya mai mulki a kasar Indiya a kan yin fitsari a titi, duk da kokari da gwamnati take yi wajen jayo hankalin ...
Rating :
5