Rundunar 'yan sandan birnin tarayyar Najeriya Abuja ta shigar da karar da Maryam Sanda da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka, a gaban kotu.
A wata sanarwar da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce ta shigar da karar Maryam Sanda ne gaban kotu ta 32 ta birnin tarayyar Najeriya, bisa tuhumar ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello Halliru.
A cikin sanarwar, rundunar ta ce abun da ake tuhumar Maryam Sanda da shi laifi ne a karkashin dokar kundin hukunta laifuka na Najeriya sashe na 221.
Sanarwar, wadda jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan birnin Abuja, Anjuguri Jesse Manzah, ya sanya wa hannu, ta ce rundunar 'yan sandan ta samu damar ajiye Maryam Sanda na mako biyu domin ta samu ta kammala bincike game da kisan kan.
Har ila yau rundunar 'yan sandan Abujan ta ce ta nemi damar rike Maryam Sanda ne domin tana da jaririya 'yar wata shida, lamarin da zai sa ya yi mata wuya ta zauna a gidan yari, har zuwa lokacin da za a saurari karar.
Sanarwar ta ce sai an kammala binciken ne sannan za a gano cewa ko za a iya sauya tuhumar da ake mata ko kuma za a tuhumi wasu mutanen daban da ake zargin tare suka aikata laifin da Maryam.
An kashe Bilyaminu Bello Halliru ne ranar 19 ga watan Nuwamba, kuma mutuwarsa na jan hankalin mutane da dama shafukan sada zumunta a Najeriya.
Source: BBC Hausa
Title :
Anshigar Da Kara Kan Matan Data Kashe Mijinta A Abuja
Description : Rundunar 'yan sandan birnin tarayyar Najeriya Abuja ta shigar da karar da Maryam Sanda da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar daba masa...
Rating :
5