Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke wasu dalibai bakwai na Kwalejin Fasaha ta Ungogo, wadanda ake zargi da halaka wani abokin karatunsu da ke ajin karshe.
Daliban dai kamar yadda `yan sanda suka ce suna zargin marigayin ne da yin luwadi.
Mahaifin mamacin, Mallam Ali Sango ya nemi hukuma da ta bi masa hakkin jinin dansa Muhammad Ali Sango, dalibin Kwalejin Fasaha ta Ungogo da ke jihar Kano.
An dai samu wasu jawabai daban-daban dangane da sanadiyyar ajalin dalibin.
Amma cikin tsananin kaduwa da juyayi, Mallam Ali Sango ya mini bayanin yadda ya samu labarin rasuwar dan nasa: "Shugaban makarantar ne yayi min waya, yace in same su maza-maza a asibitin Waziri Gidado".
Ya kara da cewa bayan ya isa asibitin, sai shugaban makarantar ya shaida masa cewa dan nasa, "ba shi da lafiya, kuma sun kawo shi asibiti amma Allah Yayi masa rasuwa. Kuma wai rashin lafiyar sakamakon ya je sayan kati masu satar waya suka lakada masa duka".
Yace yana fatan hukuma za ta dau mataki, "ta nema mana hakkin wannan yaro da aka kashe babu gaira, babu dalili".
Rundunar `yan sanadan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar dalibin. Amma binciken rundanar, kamar yadda kakakinta, DSP Magaji Musa Majiya ya ce ya saba da labarain da aka ba wa mahaifin marigayin:
"Bincike dai ya tabbatar mana cewa marigayi Muhammd Ali Sango, shekararsa 17, kuma dalibai a tsakaninsu suna zarginsa da neman maza".
Ya kara da cewa, "Haka ne yasa wasu daga cikin daliban suka hada kwarya-kwaryar yadda zasu hukunta shi".
DSP Majiya ya fada wa BBC cewa, "Yanzu akwai mutum bakwai a hannunmu, kuma a cikin mutum bakwan nan, akwai mutum hudu wadanda da su aka yi wannan dukan".
A kwalejin Fasaha ta Ungogon, shugabannin makarantar sun ce an yi wa bakinsu sakata dangane da zargin cewa dalibai na yin gaban-kansu, suna yanke irin wannan hukunci.
Ahmad Tijjani Abdullahi shi ne sakataren Hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, kuma yace ana cigaba da bincike a kan lamarin.
"Akwai wani dan littafi wanda muke rabawa dalibai a makarantu, wanda yake rayuwar daliban gaba daya mu'amularsu a kansa ta dogara", inji shi.
Ya ce "abin da bincike ya bayyanar shi ne zamu yi aiki a kansa".
A watan Agustan da ya wuce ma `yan sanda a jihar Jigawa mai makwabtaka da Kano sun kama wasu dalibai 15 na makarantar sakandare ta Karkarna bisa zarginsu da kashe wani dan makarantar tasu da shi ma suke zarginsa da yin luwadi.
Source: BBC Hausa
Title :
Ankashe Wani Dalibi Kan Zargin Luwadi A Kano
Description : Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke wasu dalibai bakwai na Kwalejin Fasaha ta Ungogo, wadanda ake zargi da halaka wani abokin karatunsu da...
Rating :
5