Wani babban jami'i a Iraki ya ce an gano wasu manyan kaburbura wadanda suke dauke da gawarwwakin mutane 400 a wani wuri da ke kusa da garin Hawija, inda a nan ne aka fatattaki mayakan kungiyar IS a makon daya gabata.
Gwamnan yankin Kirkuk ya ce an gano ramukan ne a sansanin sojin sama da ke arewacin Iraki.
Ya ce wasu daga mutanen da aka kashe na sanye ne da tufafin wandanda mayakan IS suka yanke ma hukunci kisa, ya yinda sauran na sanyene da tufafi fararen hula.
Sojoji Iraki sun gano gomman kaburbura a wasu yankuna , wadanda a baya suke karkashin ikon mayakan IS.
Lamarin na zuwa ne bayan da sojojin Iraki suka kaddamar da farmaki domin sake kwato garin Rawa, wanda shi ne gari na karshe da ke karkashin ikon mayakan IS.
Garin da kuma wasu filaye sun kasance karskashin ikon IS bayan da sojoji Iraki suka kwace garin al Qaim daga hannunsu a makon daya gabata.
Source: BBC Hausa
Title :
Angano Ramuka Dauke Da Gawawwaki A Iraki
Description : Wani babban jami'i a Iraki ya ce an gano wasu manyan kaburbura wadanda suke dauke da gawarwwakin mutane 400 a wani wuri da ke kusa da ga...
Rating :
5