Sashen bincike kan aikata kisan kai na rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya fara bin diddigin zargin aikata kisan kai da ake yi wa wata mata Maryam Sanda da rahotanni suka ce ta daɓa wa mijinta wuka sau da dama a karshen makon jiya.
Mai magana da yawun rundunar shiyyar Abuja, Anjuguri Jesse Manza ya tabbatarwa da BBC cewa suna tsare da Maryam Sanda, kuna a yanzu jami'ai suna kan binciken zargin daɓa wa mai gidanta, Bilyaminu Bello wuka a sassan jiki.
Ya ce: "rundunar ba za ta so yin azarɓaɓi ba, tun da jami'anta suna kan bincike don haka sai a bari har sai sun kammala don jin abin da ake ciki."
Rahotanni sun ce lamarin wanda ya faru ranar Asabar, ya samo asali ne bayan matar ta ga sakonnin wata mace a wayar mijinta, abin da ya sa ta dugunzuma har ta kai ga caka masa wukar da ta zama ajalinsa.
An ce al'amarin ya faru ne a gidan ma'auratan da ke unguwar Maitama a Abuja kuma tuni aka yi marigayin jana'iza, a cewar kafofin yada labaran Najeriya.
Kimanin shekara biyu kenan da yin auren kuma har A... ya albarkace su da samun 'ya mace.
BBC ta ji ra'ayoyin wasu mata kan wannan al'amari, inda ta farko ta ce "abin da ya kamata mata mu rika yi shi ne mu kau da idonmu cewa mazanmu na yi. Idan har kin san mijinki yana yin irin wannan halayya amma kika dauke ido, to za ki zauna lafiya."
Wata kuma tambaya ta yi cewa: "Ni, ina ruwana da wayarsa? Amma duk abin da mutum ya je ya gani ai shi ya janyo wa kansa, kuma ka je ka yi masa magana idan maras mutunci ne, ya gwale ka.
"Mai mutunci ne ma zai ce zo ki zauna, ya yi miki bayani...Don haka kawai mata mu dinga bin mazajenmu da addu'a."
Sai kuma wata da ke cewa: "Gaskiya na kadu sosai da na samu wannan labari. Da farko, da ma dai addini ya hana bincike. Ko wasika ce a cikin waya ko kuma a takarda a ninke, babu dalilin da zan je ina bincikawa.
"Idan ma wata kaddara ta sa kin ci karo da wani abu a wayar mijinki, Allah ya kaddara kin gani ko kuma garin bincike ne, to ni a ganina ka yi kamar ba ka gani ba," in ji ta.
Source: BBC Hausa
Title :
Anfara Bincike Kan Matan Data Cakka Wa Mijinta Wuka
Description : Sashen bincike kan aikata kisan kai na rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya fara bin diddigin zargin aikata ki...
Rating :
5