A Najeriya, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, wato EFCC, ta rungumi wata sabuwar dabara ta amfani da mawakan Kannywood don shelar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin mata da yara.
Hukumar ta yi wani gangami a Kano, inda fitattun mawaka suka nuna basirarsu wajen isar da sakon hukumar ta hanyar waka.
EFCC dai, ta bayyana cewa shigar da mata da yara a cikin yaki da cin hanci na da muhimmanci sakamakon matsayinsu a tsakanin al`uma kasancewar mata sune ginshikin tarbiyya ga yara da ake fatan su ne manyan gobe.
Dr Adamu Hamisu Danmusa, shi ne Daraktan ayyuka na hukumar EFCC mai kula da shiyyar arewa maso yamma ya ce, sun yanke shawarar fara amfani da mawaka ne domin isar da sakon da suke son isarwa ga al'umma musamman mata da yara a kan illar cin hanci.
Daraktan ya ce, mawaka ba bu inda ba sa isar da sako ta hanyar waka, don haka suke ganin amfani da mawakan zai taimaka wajen isar da sako ga al'umma, domin ba sai a rinka hada taruka don fadakar da mutane illar cin hanci ba.
Dr Adamu, ya ce dama an san mata da son waka, to ta hanyar waka za su isar da sakonni da dama.
A Najeriyar dai ana kukan cewa babu wani bangaren rayuwa da cin hanci bai ratsa ba.
Najeriya dai kasa ce mai arzikin man fetur tun farashi na ganiyarsa, da wasu muhimman albarkatun kasa, ga kuma yawan jama`a, amma duk da haka galibin al`ummar kasar na fama da talauci sakamakon cin hanci da rashawa.
Kodayake gwamnatin shugaba Buhari ta yi alwashin yaki da wannan annoba.
Source: BBC Hausa
Title :
Anfara Amfani Da Waka Wajen Yaki Da Cin Hanci
Description : A Najeriya, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, wato EFCC, ta rungumi wata sabuwar dabara ta amfani da mawaka...
Rating :
5