Ta leko ta koma ga wasu mutane kimanin 30 wadanda aka dauka aiki a asibitin kashi na Dala da ke birnin Kanoa arewacin Najeriya.
An dai janye matakin ba su aikin ne bayan da aka yi masu gwaje-gwajen shan miyagun kwayoyi kuma aka gano suna shan muggan kwayoyin.
Suna dai cikin mutum kimanin 150 da aka dauka aikin jinya a asibitin, daga cikin dubban mutane da suka nemi aikin.
Gwajin shan muggan kwayoyi dai ba wajibi ba ne ga masu neman aiki a fadin Najeriya.
Sai dai kuma daraktan watsa labarai na asibitin kashin na Dala Tijjani Musa Muhammad, ya shaida wa BBC cewa, asibitin ya dauki matakin gwajin shan kwayar ne a daukar aiki na baya-bayan nan, saboda a tabbatar an dauki ma'aikatan jinya masu cikakkiyar lafiyar kwakwalwa, saboda yadda aikin likita ke bukatar taka tsan-tsan da kuma nutsuwa.
"Yanzu idan aka ce an dauki mai tu'ammali da shan kwaya, ai ka ga akwai hadari ga su kansu marasa lafiyar.," in ji shi.
Ya ce ba zai iya tabbatar da adadin sabbin ma'aikata da ba a ba su aikin ba, saboda samun su da shan kwaya.
Amma dai wasu majiyoyi a asibitin sun ce sabbin ma'aikatan da al'amarin ya shafa sun kai 30.
Kawo yanzu dai hukumomin ba su bayyana irin kwayoyin da aka gano mutanen suna tu'ammali da su ba.
Rahotanni sun ce sabbin ma'aikatan wadanda galibinsu matasa ne da suka kammala karatun jami'a sun fusata da aka shaida musu cewa ta-leko-ta-koma, saboda suna shan miyagun kwayoyi.
Asibitin kashi na Dalan ya ce a halin yanzu ma yana fama da wasu ma'aikatan biyar, wadanda aka dauka aiki a can baya, kuma suke fama da tabin hankali, ga alama sanadiyyar shan muggan kwayoyi.
Jihar Kano, wadda ita ce jiha mafi yawan jama'a a Najeriya ce kan gaba wajen shan muggan kwayoyi a kasar, a cewar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA.
Source: BBC Hausa
Title :
Andauki Matasa Aikin Asibiti A Kano Saboda Shan Kwaya
Description : Ta leko ta koma ga wasu mutane kimanin 30 wadanda aka dauka aiki a asibitin kashi na Dala da ke birnin Kanoa arewacin Najeriya. An dai jany...
Rating :
5