An bude babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a tsakiyar Najeriya, bayan masu zanga-zanga sun rufe ta har na tsawon sa'o'i hudu ranar Lahadi.
Wasu mazauna kauyen Sabon Gayan da ke kusa Kaduna sun rufe hanyar ce daga misalin karfe 1:00 zuwa 4:00 na yamma, bayan wasu da ake zargin barayi ne sun kashe wani shugaban matasan yankin.
Mutanen sun ce sun dauki matakin ne saboda yadda "masu garkuwa da mutane suke cin karensu babu babbaka a yankin."
Rahotanni sun ce dubban ababan hawa ne suka yi cirko-cirko a kan hanyar, kafin daga bisani jami'an tsaro su yi nasarar tarwatsa masu zanga-zangar.
Wani matafiyi, Muhammad Isa, wanda ke wurin ya shaida wa BBC cewa masu zanga-zangar sun kwashe sa'o'i a kan hanyar.
Mai bai wa gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Sama'ila Yakawada, wanda shi ma lamarin ya rutsa da shi, ya tabbatar wa BBC faruwar al'amarin.
Kuma ya ce akwai mutum guda da ya rasa ransa yayin da jami'an tsaro suke kokarin karbe iko da hanyar daga hannun masu zanga-zangar.
Source: BBC Hausa
Title :
Anbude Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Description : An bude babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a tsakiyar Najeriya, bayan masu zanga-zanga sun rufe ta har na tsawon sa'o'i hudu ranar Laha...
Rating :
5