Ministocin gwamnatin Afirka Ta Kudu suna birnin Harare don tattauna wa da hambararren shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, kan rikicin da ke faruwa a kasar.
Suna kokarin cimma wata yarjejeniya ce a kan makomar Zimbabwe da kuma mutumin da ya jagoranci kasar tsawon shekara 37, wanda a yanzu kuma yake fuskantar talala.
Nan ba da jimawa ba kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (Sadc), za ta yi wani taro na gaggawa.
Amma majiyoyi sun ruwaito cewa mai yiwuwa Mista Mugabe ya ki amincewa da matsin lambar da ake masa ya sauka.
Sun ce Mista Mugabe ya tsaya kai-da-fata cewa shi ne halattaceen shugaban kasa.
Haka kuma, shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU, wato shugaba Alpha Conde na Guinea, ya ce AU za ta taba amincewa da kwace iko da sojoji suka yi ba.
Ya ce yana gayyatar sojojin da su koma sansaninsu su kuma dawo da dokar kundin tsarin mulki.
Rashin tabbas
An shiga halin rashin tabbas game da makomar shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe yayin da sojin kasar ke ci gaba da yi masa daurin talala a gidansa.
Ga 'yan Zimbabwe da dama, yiwuwar barin mulkinsa, abin marhabin ne, ko da yake, suna guna-guni, don kuwa ba su san wani shugaba sai shi tun bayan samun 'yancin kai.
Ana gudanar da tattaunawa a kasar da kuma a Botswana mai makwabtaka kan makomar Zimbabwe.
Ana tsare da wasu ministocin gwamnati yayin da manyan makusanta suka juya baya ga matarsa Grace Mugabe wadda tashen kasaitarta ya janyo wannan matakin soja.
Wakiliyar BBC ta ce ko da yake, Mista Mugabe ya kubuce wa takunkuman kassarawa da kasashen Yamma suka kakaba da kuma matsin lamba daga 'yan adawa da ke da karfi a baya, "amma sai ga shi makusantansa sun tade shi ya fadi."
Wani jagoran adawar kasar, Tendai Biti, ya bukaci sojoji su mayar da kasar kan mulkin dimokradiyya ta hanyar kafa wata hukumar wucin gadi da za ta yi jagora zuwa zabe.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Tattaunawa Kan Makomar Zimbabwe
Description : Ministocin gwamnatin Afirka Ta Kudu suna birnin Harare don tattauna wa da hambararren shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, kan rikicin da ke far...
Rating :
5