Ana ci gaba da nuna damuwa game da yiwuwar barkewar cututtuka sakamakon amfani da gurbatattcen ruwa a Kisangani, birni na uku mafi girma a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Tun a ranar Alhamis din data gabata ne ruwan fanfo da wutar lantarki suka yanke a birnin.
Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar ya ce, mummunan ambaliyar ruwa ce ta haddasa daukewar lantarki a babbar tashar samar da wuta.
Yanzu birnin wanda yake da mutane fiye da miliyan daya da rabi, ya dogara ne da ruwan da ba'a tace ba wanda ake debowa daga rijiyoyi da rafuka.
Rahotanni sun ce shugaban kasar Joseph Kabila, ya samar da injin din janareta wanda aka ajiye shi a babban asibitin da ke birnin, domin a samu hasken lantarki don a ci gaba da kula da marassa lafiya yadda yakamata.
Akasarin na'urori da ababan more rayuwa a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congon dai sun lalace saboda shekara da shekaru ba'a kulawa da su.
Source: BBC Hausa
Title :
Ana Fargabar Barkewar Cututtuka A Congo
Description : Ana ci gaba da nuna damuwa game da yiwuwar barkewar cututtuka sakamakon amfani da gurbatattcen ruwa a Kisangani, birni na uku mafi girma a J...
Rating :
5