An gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya cikin tsauraron matakan tsaro.
Babu wurin da aka samu rahoton tashin hankali, yayin da jama'a suka kada kuri'unsu a ranar Asabar.
Jami'an tsaro sun yi sintiri a duk fadin jihar musamman a garin Onitsha, inda kungiyar da ke fafutikar ballewa daga Najeriya IPOB da kuma kungiyar MOSSOB suke da karfi.
Jam'iyyu 37 ne za su fafata a wannan zabe mai cike da cece-ku-ce, ko da yake 'yan takarar jam'iyyu biyar ne suka yi fice wato:
Tony Nwoye na APCGwamna Willie Obiano na APGAOseloka Obaze na PDPGodwin Ezeemo PPDOsita Chidoka na UPP
Wasu mazauna garin Akwa babban birnin jihar Anambra su sun ce shirye-shirye sun kammala ta fuskar gudanar da zaben da batun sha'anin tsaro da dai sauransu.
Sai dai sun ce IPOB ta rika yada takarda da ke cewa "zabe ba zai gudana ba" .
Kugiyar ta kuma nemi mutane akan su zauna a gida, kada su fita.
Wakilin BBC ya ce zaben zai kasance zakaran gwajin dafi ga jam'iyyar APC mai mulki a yankin kudu maso gabashin kasar.
A farkon makon nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara yankin inda ya kaddamar da wasu ayyuka.
Source: BBC Hausa
Title :
An Tsaurara Tsaro A Zaben Jahar Anambra
Description : An gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya cikin tsauraron matakan tsaro. Babu wurin da aka samu rahoton t...
Rating :
5