Jam'iyya mai mulki a Zimbabwe Zanu-PF ta sauke Shugaban Kasar Robert Mugabe daga shugabancin jam'iyyar.
An kuma kori matarsa Grace da kuma wadansu daga cikin manyan jam'iyyar.
Zanu-PF ta nada Mataimakinsa Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon shugabanta.
Mista Mugabe ya kori Mnangagwa ne daga aiki kimanin makonni biyu da suka wuce.
A ranar Laraba ne sojojin kasar wadanda suke goyon bayan mataimakinsa suka yi wa Mista Mugabe daurin talala a birnin kasar Harare.
Masu zanga-zanga sun nufi fadar Shugaban Zimbabwe Shugaba Robert Mugabe don su bayyana bukatarsu ta shugaban ya sauka daga mulki a ranar Asabar.
Source: BBC Hausa
Title :
An Sauke Mugabe Daga Shugabancin Jam'iyarsa
Description : Jam'iyya mai mulki a Zimbabwe Zanu-PF ta sauke Shugaban Kasar Robert Mugabe daga shugabancin jam'iyyar. An kuma kori matarsa Grace...
Rating :
5