Wani ango a kasar Masar ya samu mummunan rauni a 'ya'yan marainansa sakamakon harbin bindiga da wani mutumin da aka gayyata bikin ya yi bisa kuskure.
Baya ga samun nakasa a 'ya'yan marainansa, angon mai suna Osman al-Alsaied, mai shekara 28 ya kuma samu jikkata a cinyarsa da hannunsa.
Ibtila'in dai ya samu Osman al-Alsaied ne a darensa na karshe na fita daga samartaka.
'Yan sanda sun ce wanda ya yi harbin, mai shekara 26 ya yi sakaci wajen rike bindigar saboda mai makon ya harbi iska sai ya harbi 'ya'yan marainan angon kai tsaye.
Kuma bayan aikata wannan danyen aiki ne sai bakon ya arce daga wurin bikin.
To amma daga baya 'yan sandan sun samu nasarar cafke shi kuma yanzu haka yana hannunsu domin amsa tambayoyi.
Wannan al'amari dai ya janyo kace-nace a shafukan sada zumunta, inda wasu suka yi ta kiraye-kirayen neman a hana irin wasan harbin bindiga lokacin bukukuwan aure.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da irin wannan abu yake faruwa a lokacin biki a Masar domin hakan ya faru a watan da ya gabata.
Sai dai kuma sabanin wancan, wani wanda ya halarci bikin ne ya samu rauni har aka yi masa tiyata.
Yanzu haka, ango Osman al-Alsaied na can kwance a asibiti domin karbar magani.
Abin da kuma mutane da dama wadanda ba 'yan Masar ba ke tambaya shi ne, ko ya ya amaryar ta ji da wannan al'amari?
Source: BBC Hausa
Title :
An Harbi Wani Ango A 'Ya'yan Maraina A Masar
Description : Wani ango a kasar Masar ya samu mummunan rauni a 'ya'yan marainansa sakamakon harbin bindiga da wani mutumin da aka gayyata bikin ya...
Rating :
5