Rundunar sojin Amurka ta haramta wa dukkan dakarunta da suke Japan shan barasa, bayan da aka samu daya daga cikinsu da hannu a wani mummunan hatsari a tsibirin Okinawa wanda yake da alaka da tuki cikin maye.
Har ila yau an umarci dakarun sojin Amurkan da su killace kansu a sansanin ko kuma a gida.
A ranar Lahadi ne sojan kundin-balar wanda ke tuka wata babbar mota ya afka wa wata karamar mota, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar direban.
Sama da rabin sojin Amurka da ke Japan ne ke zaune a Okinawa.
A wata sanarwa, rundunar sojin Amurkan ta tabbatar da cewa daya daga cikin ma'aikatanta na da hannu a afkuwar hatsarin, tare da bayyana cewa "shan barasa na iya zama abun da ya haddasa hakan."
Har ila yau sojin sun bayar da sanarwar cewa, "dole ne a bayar da horo ga dukkan dakarun sojin da suke fadin Japan game da yin ta'ammali da barasa, da kuma halaye da dabi'un da aka amince da su."
'Yan sandan sun ce sun kama shi kuma ana tuhumarsa da laifin yin tuki cikin maye wanda ya yi sanadiyyar asarar rai.
Amurka da suke Okinawa a gabashin Japan ginshiki ne na tabbatar da tsaro a tsakanin kasashen biyu. Kuma a kalla gidajen sojin Amurka 26,000 ne a tashar.
Suna shirin mayar da wasu daga cikin sojin wani bangaren, don rage yawansu a yankin tsibirin, sai dai yawancin mazaunan Okinawa sun fi son a dauke sansanin kacokam daga yankin.
A shekarar 2016 ma, an samu wani tsohon soja da yake aiki a daya daga cikin sansanonin da hannu a kisan wata mata, inda hakan ya yi sanadiyyar haramta shan barasa na wucin gadi da kuma dokar takaita zirga-zirga da daddare.
Source:BBC Hausa
Title :
An Haramta Wa Sojin Amurka Shan Giya A Japan
Description : Rundunar sojin Amurka ta haramta wa dukkan dakarunta da suke Japan shan barasa, bayan da aka samu daya daga cikinsu da hannu a wani mummunan...
Rating :
5