Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta amince Audu Maikaba ya zama kocin matasa 'yan kasa da shekara 17 da ake kira Golden Eaglets.
Kwamitin tsare-tsare da ci gaban kwallon kafar Nigeria ne ya yi bitar kwazon kocin, sannan ya bayar da shawarar da a danka wa Maikaba aikin horar da matasan na Nigeria.
Audu Maikaba tsohon kocin Kano Pillars da Enyimba, ya jagoranci Akwa United ta ci kofin kalubalen Nigeria na bana, sannan kungiyar ta yi ta hudu a gasar Firimiya da aka kammala.
Maikaba zai yi aiki da Abubakar Bala da Oluwafunsho Bunmi Haruna a matsayin mataimaka da kuma Baruwa Abiodeen a matsayin mai horar da masu tsaron ragar tawagar.
Super Eagles ta kasa kai wa gasar cin kofin duniya da aka yi a China, inda Ingila ta lashe kofin a karon farko a tarihi.
Source: BBC Hausa
Title :
An Baiwa Wa Audu Maikaba Golden Eaglet
Description : Hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF ta amince Audu Maikaba ya zama kocin matasa 'yan kasa da shekara 17 da ake kira Golden Eaglets. Kw...
Rating :
5