Tsoffin kawayen shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, sun yi kakkausar suka ga matakin da ya dauka na yin biris da kiraye-kirayen da ake masa a kan ya yi murabus.
Shugaban kungiyar 'yan mazan jiya, Chris Mutsvangwa, ya shaida wa BBC cewa, an riga an gama da Mr Mugabe a fagen siyasa domin babu wani tasiri da zai yi.
Mai magana da yawun jam'iyyar kasar mai mulki ta Zanu-PF ya ce, yanzu Mr Mugabe ba shi da wani iko.
Jam'iyyar wadda tuni ta cire shi daga shugabancinta, ta ba shi wa'adin nan da karfe 12 ranar Litinin ya yi murabus, ko kuma a tsige shi.
Har ila yau jam'iyyar ta kuma kori matarsa Grace, da kuma wadansu daga cikin manyan jam'iyyar.
Kuma jam'iyyar ta nada mataimakinsa Emmerson Mnangagwa, a matsayin sabon shugabanta.
Za a fara muhawara kan batun tsige shi din a majalisar dokokin kasar a ranar Talata.
Mr Mutsvangwa ya ce kungiyarsu za ta tabbatar Mr Mugabe ya sauka idan har jam'iyyarsa ta gaza tsige shi.
Ya ce: "Kamar yadda kuka sani jam'iyyarsa ta sanar da shi ya yi murabus kafin sha biyun rana, idan har ya ki kuwa, to za a fara daukar matakan tsige shi.
Me ya Mugabe ya fada a jawabinsa?
A jawabin da ya gabatar ga al'ummar kasar ta gidan talabijin ranar Lahadi, Mista Mugabe ya ce shi zai jagoranci babban taron jam'iyyarsa ta Zanu-PF wanda za a yi a watan gobe.
Shugaba Mugaben ya ce zai jagoranci babban taron jamiyyar Zanu PF da za a yi a watan gobe.
Ya kuma yi gargadi a kan kada mutane su dauki mataki na ramuwar gayya akan magoya bayansa.
Sannan ya ce yana mutukar farin ciki game da yadda aka rika tafiyar da harkokin gwamnati ba tare da wata matsala ba.
Mugabe ya ce yana sane da masu adawa da shi a cikin jam'iyyar Zanu-PF da rundunar sojin kasar da kuma al'ummar kasar, inda ya ce akwai bukatar dawo da Zimbabwe kan hanya.
Jawabin Robert Mugabe
Karfin ikon Mista Mugabe ya fara raguwa ne a ranar Laraba, kan batun wanda zai gaje shi.
Rikicin ya samo asali makonni biyu da suka wuce bayan Mista Mugabe, mai shekara 93, ya kori Mista Mnangagwa daga aiki.
Abin da ya sa tsofaffin kwamandodin sojojin kasar suke ganin wani yunkuri ne na share wa matarsa hanyar maye gurbinsa.
A ranar Laraba ne sojojin kasar wadanda suke goyon bayan mataimakinsa suka yi wa Mista Mugabe daurin talala a birnin kasar Harare.
Masu zanga-zanga sun nufi fadar Shugaban Zimbabwe Shugaba Robert Mugabe, don su bayyana bukatarsu ta shugaban ya sauka daga mulki a ranar Asabar.
Source: BBC Hausa
Title :
An Baiwa Mugabe Waadin Sauka Mulki Ko A Tsigeshi
Description : Tsoffin kawayen shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, sun yi kakkausar suka ga matakin da ya dauka na yin biris da kiraye-kirayen da ake ma...
Rating :
5