Kyatin din Barcelona Andres Iniesta ya sanya hannu a yarjejeniyar zama a kungiyar har abada.
Dan wasan kasar Spain din ya yi wa Barcelona wasa sau 639 wanda shi ne na biyu a jerin tarihin 'yan wasan da suka fi taka wa kungiyar teda, inda ya yi nasarar zura kwallaye 55 a raga.
Iniesta ya je kungiyar ne a shekarar 1996 lokacin da yake da shekara 12 da haihuwa.
Ya fara taka leda ne a watan Oktobar shekarar 2002, kuma ya yi nasarar lashe Kofin Zakarun turai har sau hudu.
Dan wasan gaban ya zama kyatin din kungiyar ne a shekarar 2015 kuma kofuna 30 ya lashe a tarihin zamansa a kungiyar, kamar dai takwaransa Lionel Messi.
A wata sanarwa da Barcelona ta fitar ta ce: "Andres Iniesta ya sanya hannu a yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar har karshen rayuwarsa ta kwallon kafa a ranar Juma'a."
Source: BBC Hausa
Title :
Zanci Gaba Da Zama A Barcelona Har Abada-Iniesta
Description : Kyatin din Barcelona Andres Iniesta ya sanya hannu a yarjejeniyar zama a kungiyar har abada. Dan wasan kasar Spain din ya yi wa Barcelona w...
Rating :
5