Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya yi kira ga mutane a kan su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kuma su kada kuria a zaben shugaban kasa da za a sake yi a yau .
Mista Kenyatta ya ce an tura da jamian tsaro zuwa sasan kasar daban-daban kuma ya yi gargadin cewa ba zai amince da tashe tashen hankula ba.
Jagoran 'yan hammaya, Raila Odinga , ya nemi magoya bayansa a kan su kauracema zaben , saboda ya yi ammanar cewa ba sahihin zabe bane.
Zaben zai gudana ne bayan da kotun koli ta kasa saurarar karar da wasu suka shigar a gabanta, inda suka nemi a dage zaben.
An yi taho-mu-gama tsakanin 'yan sanda da magoya bayan Mista Odinga a lardin Kisumu.
Gwamnatin kasar ta bada hutu a jiya Laraba domin mutane su samu damar yin tafiya zuwa wuraren da aka yi mu su rajista.
Zaman doya da manya da ake yi tsakanin 'yan siyasa na janyo fargaba kan barkewar tashe tashen hankula.
Mutum fiye da 1'600 ne suka mutu ya yinda dubai sun rasa matsugunansu a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi a 2007.
Source: BBC Hausa
Title :
Zaben Shugaban Kasar Kenya
Description : Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya ya yi kira ga mutane a kan su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu kuma su kada kuria a zaben shugaban kasa d...
Rating :
5