Kasar Saudiyya na yin wani gagarumin aikin gyara rijiyar Zamzam a babban Masallacin Haram da ke birnin Makkah.
Babban mai kula da Masallatan Makkah da Madinah, Sheikh Abdulrahman Al-Sudais wanda ya sanar da fara aikin, ya ce za a fadada girman rijiyar tare da tsabtace kewayanta.
Miliyoyin mahajjata ne ke amfani da ruwan Zamzam a Masallacin Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad SAW da ke Madina.
Musulmi na dibar ruwan a ko wanne lokaci zuwa kasashensu.
Sun yi amannar cewa rijiyar samuwarta daga Allah ne, wacce ta samar da ruwa don kashe kishirwa lokacin da Annabi Ibrahim AS ya bar matarsa da dansa a cikin Sahara.
Sarki Salman ne ya amince da aikin gyara rijiyar da za a kwashe watanni bakwai ana yi.
Sheikh Abdulrahman Al-Sudais ya ce ana sa ran kammala gyaran kafin watan Ramadan mai zuwa.
An dai yi amannar cewa rijiyar Zamzam da ke kusa da Ka'aba, ita ce rijiyar da ta fi ko wacce dadewa a duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Zaa Fadada Rijiyar Zam Zam A Masallacin Makkah
Description : Kasar Saudiyya na yin wani gagarumin aikin gyara rijiyar Zamzam a babban Masallacin Haram da ke birnin Makkah. Babban mai kula da Masallata...
Rating :
5