Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Kwamred Adamu Ango, ya ce yawancin malaman makarantar firamaren jihar sun ci jarabawar da gwamnatin jihar ta yi musu a kwanakin baya.
Gwamnatin jihar ta jaraba malaman firamare 33,000, inda ta ba su jarabawar dalibai 'yan aji hudu.
Sai dai kashi 66 cikin 100 na malaman sun fadi jarabawar, a cewar gwamnatin jihar, inda ta ce malamai 21,780 ba su samu maki 75 cikin 100 ba.
Kwamred Ango ya ce sun samu rahoton wucin gadi wanda ya nuna cewa "kashi 73.3 cikin 100 na malaman da suka zauna a jarabawar ne suka yi nasara."
Ya ci gaba da cewa "wadanda suka samu maki 60 cikin 100 ke nan. To me ya sa kuma za a juya a ce sai kawai wadanda suka ci maki 75 cikin 100 ne suka ci."
Sai dai Mai Magana da yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan ya musanta hakan, inda ya ce kamata ya yi "idan malami yana koyar da darasi, ya ci maki 75 cikin 100 a jarabawar darasin."
Source: BBC Hausa
Title :
Yawancin Malaman Firamarin Kaduna Sunci Jarabawarsu-Kungiyar Kwadago
Description : Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Kwamred Adamu Ango, ya ce yawancin malaman makarantar firamaren jihar sun ci jara...
Rating :
5