Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar harin da bam din da aka kai birnin Mogadishu na kasar Somaliya ya kai 358, kamar yadda ministan yada labaran kasar Abdirahman Osman ya bayyana.
Akwai kimanin wadansu mutum 56 da har yanzu ba a san inda suke ba, kamar yadda ministan ya ce.
Hukumomin kasar sun dora alhakin harin a kan kungiyar al-Shabab. Amma kungiyar ba ta ce ita ta kai harin ba.
Wata babbar mota ce da aka sanya wa bama-bamai ta fashe da su a wani wuri mai hada-hadar jama'a, inda ta lalata wadansu otels da gine-ginen gwamnati da kuma gidajen cin abinci.
Bama-baman sun tashi kusa da wata motar tanka abin da ya sa mummunan gobara ta tashi nan take.
Harin ya jikkata mutum 228, wadanda 122 daga cikinsu kuma an garzaya da su kasashen Turkiyya da Sudan da kuma Kenya don yi musu magani, a cewar Mista Osman.
An bukaci 'yan kasar da su ba da gudunmuwar jini a asibitoci.
Fiye da mutum 150 cikin mutanen da suka mutu sun yi mummunar kuna ne kuma gwamnati ta sa an binne su a ranar Litinin.
Daruwan 'yan kasar ne suka yi zanga-zanga don yin Allah-wadai da kungiyar al-Shabab bayan harin, inda galibinsu suke sanya jan kyalle a goshi don nuna aihini ga wadanda harin ya shafa.
Akwai dakarun kungiyar Tarayyar Afirka 22,000 a kasar wadanda suke taimaka wa gwamnatin kasar wajen sake kwato yankunan da ke hannun al-Shabab, wadanda suke da tasiri a yankunan karkarar kudancin kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Yawan Wadanda Aka Kashe A Harin Mogadishu Ya Kai 358
Description : Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar harin da bam din da aka kai birnin Mogadishu na kasar Somaliya ya kai 358, kamar yadda ministan yada ...
Rating :
5