Daruruwan 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Sheikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja domin neman gwamnati ta saki malamin.
Baya ga haka 'yan kungiyar sun nuna adawa da yunkurin gwamnatin kasar na sa kwamitin da zai binciki abin da ya faru tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar a garin Zariya a shekarar 2015 yayi zama a asirce.
Rikicin dai ya haddasa asarar rayuka da dama, kuma tun lokacin ne ake tsare da malamin duk kuwa da umarnin kotu na a sake shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Shi'a Na Gudanar Da Zanga Zangan Sako Zakzaky
Description : Daruruwan 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Sheikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da wata zanga-zanga a Abuja domin neman gwamnati ta ...
Rating :
5