Akalla mutum 30 ake zargin 'yan sanda suka kashe yayin wata zanga-zanga da 'yan adawa suka yi a birnin Nairobi na kasar Kenya.
A wani sabon rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar ta ce 'yan sandan kasar ''suna da hannu dumu-dumu''.
Har ila yau, akwai wadansu rahotanni da ba a tabbatar ba wadanda suke cewa 'yan sandan sun kashe wadansu mutum 17 a birnin.
Suna zargin 'yan sandan da tayar da zaune tsaye ta amfani da karfin da ya wuce kima a yankunan da ake tunani cewa ana tashin hankali.
Kungiyar ta ce 'yan sandan sun yi amfani da karfin da ya wuce kima ne a wuraren da ake zaton rikici.
A makon da ya gabata ne jagoran 'yan adwar kasar, Raila Odinga, ya ce ba zai shiga zaben sugaban kasa da za'a sake yi a cikin wannan watan.
Saboda ba shi da imanin cewa za a yi zabe adalci a zabe, a cewarsa.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Sanda Sunkashe Masu Zanga Zanga Mutum 30
Description : Akalla mutum 30 ake zargin 'yan sanda suka kashe yayin wata zanga-zanga da 'yan adawa suka yi a birnin Nairobi na kasar Kenya. A wa...
Rating :
5