Yan majalisar kasar Uganda sun mayar da dala 8,000 kimanin fam 6,000 da aka ba kowannensu domin tsawaita mulkin shugaba Yoweri Museveni.
Shugaba Museveni ya shafe shekara 31 yana mulkin Uganda.
'Yan majalisun su takwas sun mayar da fam 8,000 da kak bai wa kowannensu domin su tuntubi al'umominsu game da wani kuduri mai cike da takardama na tsawaita wa'adin shugaban kasa.
'Yan adawa a kasar sun soki wannan lamarin, suna cewa "cin hanci da rashawa" ne, saboda 'yan majalisar sun riga sun ziyarci mazabunsu.
Ana kallon wannan a matsayin wani yunkuri na zawarcin 'yan majalisar domin su cire wani sashe na dokar kasar da ya hana duk wanda shekarunsa suka wuce 75 daga takarar shugabancin kasar.
'Yan adawar na ganin jam'iyyar shugaban kasa Museveni na neman tsawaita mulinsa ne a fakaice. Shekarun shugaba Yoweri Museveni na da shekara 73 da haihuwa ne a halin yanzu.
Za a gudanar da zaben shugaban kasar Yugandan ne dai a shekarar 2021, kuma wa'adin shugabancin kasar ta Uganda shekara 6 ne.
Jam'an majalisar sun bayyana cewa an ware dala miliyan 3.5 domin 'yan majalisar kasar su tuntubi jama'arsu dangane da wannan kudurin dokar.
Ko wane dan majalisa zai karbi dala 8,000 domin aiwatar da wannan aikin cikin mako biyu masu zuwa.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Majalisa Sun Mayar Da Cin Hancin $8,000
Description : Yan majalisar kasar Uganda sun mayar da dala 8,000 kimanin fam 6,000 da aka ba kowannensu domin tsawaita mulkin shugaba Yoweri Museveni. Sh...
Rating :
5