Wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a kusa da ofishin hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka ce.
Sai dai a cewar shugaban hukumar Injiniya Satomi Ahmad, 'yar kunar bakin waken ce kawai ta rasa ranta a lamarin wanda ya faru da yammacin Asabar.
Mutum 14 ne suka mutu a makon jiya baya ga 'yan kunar-bakin-wake uku sanadiyyar wani harin da aka kai Muna Garage a wajen birnin Maiduguri.
Source: BBC Hausa
Title :
Yan Kunan Bakin Wake Sunkai Hari Maiduguri
Description : Wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a kusa da ofishin hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke Maiduguri a arewa ...
Rating :
5