Gwamnatin Spaniya ta yi watsi da kiran da jagoran 'yan yankin Catalonia na kasar Carles Puigdemont, ya yi domin tattaunawar sasanta rikicin da ya taso kan neman 'yancin da yankin ke yi.
Ofishin Firamininistan kasar, Mariano Rajoy, ya ce, ko alama gwamnati ba za ta lamunci abin da ta kira yaudara da bata suna ba.
Yayin da lokaci ke kara matsowa na aiwatar da ikirarin da jagororin yankin na Catalonia ke yi na ayyana 'yancin kai a mako mai zuwa, gwamnatin Spaniya na nan daram a kan matsayinta na adawa da hakan.
Matsayin gwamnatin na Spaniya shi ne kuri'ar rafarandan ta neman ballewa daga kasar da aka yi a yankin na Catalonia ranar Lahadi, ta saba wa tsarin mulkin kasar, kuma kotunan kasar sun ayyana ta a matsayin wadda ta saba wa doka, sannan ba ta da wani tasiri a hukumance.
Gwamnatin kasar ta Spaniya, ta ce ba za ta tattauna a kan abin da ya saba wa doka ba, ko ta lamunta da yaudara ko batanci ba.
Gwamnatin ta kara da cewa idan har Mista Puidgemont na son a sasanta, to sai ya koma ga doka, wato ya yi watsi da batun ayyana 'yancin Catalonia.
Gwamnatocin wasu kasashen na Turai sun mara baya ga takwararsu ta Spaniya da cewa dole ne a bi abin da doka ta tanada.
Source: BBC Hausa
Title :
Yakin Neman 'Yan Cin Catalonia Ta Kara Cabewa
Description : Gwamnatin Spaniya ta yi watsi da kiran da jagoran 'yan yankin Catalonia na kasar Carles Puigdemont, ya yi domin tattaunawar sasanta riki...
Rating :
5