Uwargidan tsohon shugaban Najeriya, Patience Jonathan, ta ce hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa na yi mata 'bi-ta-da-kulli.'
A wata sanarwar da mai magana da yawunta, Belema Meshack-Hart, ya fitar, wacce jaridun kasar da dama suka buga, Misis Jonathan ta zargi hukumar da yi mata rashin adalci, tana mai cewa ba bu wata uwargidan shugaban kasa da aka taba yi wa irin barazanar da ake yi mata a tarihin kasar.
Misis Jonathan ta yi kira ga Shugaba Buhari da ya ja kunnen Shugaban EFCC Ibrahim Magu domin hukumar ta dakatar da binciken da take yi mata.
Ta zargi gwamantin Buhari da yi wa kungiyarta ta tallafa wa jama'a binciken kwa-kwaf sabanin yadda ta kyale sauran kungiyoyin matan tsaffin shuwagabannin kasar.
Madam Patience ta ce ana bincikarta ne saboda "rawar da ta taka a lokacin yakin neman zaben 2015", tana mai cewar mijinta bai dauki mataki kan matar Buhari ba kan rawar da ta taka a zaben shekarar 2011.
Kazalika ta ja hankalin Shugaba Buhari da ya dubi yadda Shugaba Trump na Amurka bai shiga harkar matar tsohon shugaban kasar ba Michelle Obama ba, duk da rawar da ta taka a zaben kasar na bara.
A baya dai, hukumar EFCC ta dakatar da wasu asusun Misis Jonathan na banki,kuma uwargidan tsohon shugaban kasar ta samu hukuncin kotun wanda ya sa hukumar ta sakammata asusun nata.
Gwamnatin Shugaba Buhari dai tana zargin da dama daga cikin tsaffin jami'an gwamnatin Goodluck Jonathan da wawushe dukiyar kasa.
Zargin da yawansu suka sha musantawa da cewa siyasa ce kawai.
Kawo yanzu dai gwamnatin Shugaba Buhari da hukumar EFCC ba su mayar da martani kan kalaman da Patience Jonathan ta yi ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Yakamata Buhari Yaja Kunnen Magu-Patience Jonathan
Description : Uwargidan tsohon shugaban Najeriya, Patience Jonathan, ta ce hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa na yi mata 'bi-ta-da-kulli....
Rating :
5