Cikin Disambar 2015 aka rika samun tsilli-sillin matsaloli a sassan Amurka. Ba su da yawa a lokacin, amma suna faruwa akai-akai, inda wadanda suka jikkata alamun cutarsu ke nuni da amai da zawayi mai jini, kuma gwajin da aka yi musu ya tabbatar suna dauke da kwayar cutar E. coli.
Kuma wadannan majinyata akwai su kusan ko'ina, inda aka samu aukuwar cututttuka a jihohi 20 daidai lokacin da cibiyoyin shawo kan cututtuka suka bayyana barkewar annobar, daidai lokacin da aka kai mutum 10 asibiti.
An fahimci cewa kwayar cutar E.coli na damfare ne a abin da suka ci, kuma cibiyoyin tarairayar cututtukan na CDC, da ke aiki tare da kananan hukumomin kula da lafiya da na jihohi, suka sanya masu bincike su shawo kan al'amuran.
Yayin da mutane da yawa ba su san cewa guba kadan a cikin abinci na iya yin mummunar illa, kuma ba a al'amari da yake a kebe ba. A mafi munin lamuran har kisa take yi.
Don gano tushen asalin yaduwar cutar sai aka bi kadin gubar baibaye da mahauta ko kazantar da ta baibaye tsirrai, ta yadda in an bi misali sai a fahimci cewa ita ce kariyarmu nan gaba.
Labarin barkewar annobar cutar E.cooli ya samu asali ne a hunturun 2015 wadda ta bude kafar barazana ga rayuka; akwakun dakin girkinka, domin aikin dubagari ya ta'allaka ne wajen tabbatar da kariyar lafiyar al'ummma, al'amarin da ke farawa daga halartar wurin da matsala ta auku nan take, tare yin tambayoyi kan lamarin.
Ko mene majinyata suka ci har suka kamu da rashin lafiya? Ko za su iya tuna abin da suka sawo daga shagon sayar da kayan masarufi a wannan makon da suka kamu rashin lafiya?
Ko sun yi matukar karakaina a shaguna sayar da kayayyaki da amfani da katin sayayya, masu bincike za su gano shagon da suka yi sayayya?
A kan ko wanne majiyaci, jami'in duba garin lafiya kan shafe mintuna 30 zuwa 40 don cike takardun tambayoyi, kamar yadda Ian Williams, shugaban reshen kawo daukin gaugawa lokacin barkewar annoba da shawo kanta na CDC ya bayyana.
Manufar dai a gano nau'ukan abincin da ke da alaka da marasa lafiyar.
A wasu lokutan sukan ci gyada da makwalashen burodi mai kakide. Ko daukacinsu sun ci kwadon ganyen salat. Saqi dai a irin wannan yanayin, cewa ya yi, "yadda managarcin tsarin bin kadin al'amaurta ta hanyar cike takardun tambayoyi bai haifar da komai ba."
Sannan akwai wasu matsalolin da ke tattare da barkewar annobar. Kimanin kashi 80 cikin 100 na marasa lafiyar mata ne.
Cigbiyar shawo kan cututtuka ta CDC ta tattara bayanan kwayoyin halittar majiyatan da suka kamu da cutar E. coli, wani kyakkyawan tsarin bin kadin al'amura da suka fito da shi, tattare da tattara bayanan kwayoyin halittar dangwala yatsu da suka kasance iri guda, ko suka kusa yin kama da dama.
Wannan na nufin cewa matsala guda ce ta haifar da daukacin cututtukan. Amma ko mene ne? A dalilin haka cututtukan suka yi ta faruwa. "Mun rika samun uku, hudu ko biyar na wadanda suka kamu da cutar daga mako zuwa mako, mako bnayan mako," in ji Williams.
Wannan bakon al'amari ne. Suna ta yawan bazuwa cikin kankanen lokaci, tamkar daukacin abin da amrasa lafiyar suka ci na haifar da matsala da ta ki ci, ta ki cinye tsawon lokaci, ko kuma sun yi ta ci akai-akai.
Tashin hankalin shi ne barkewar annobar asalinta ba daga abinci ba ne, amma an ganota a jikin kwado.
Masu binciken suna ganin masu fama da cututtukan a akwatin talabijin din na'urarsu lokacin da asibiti ko dakunan bincike suka tattara bayanai, inda aka yi gwajin burrbusshin cututttukan majiyatan kan kwayar cutar backteria.
Sannan aka dorata a shafukan sadarwar dakin bincikeen da ake kira PulseNet PulseNet nan ne inda cibiyar shawo kan cututtuka ta CDC take gane cewa an samu barkewar annoba, kuma ta sanar da su cewa annonbar na ci gaba da yaduwa. Sai dai har yanzu abin da ya haifar da ita na da rikitarwa (ko ba a gano shi ba).
Sai dai a irin wannan hali masu bincike sai sun yi amfani da basira ta musamman. Alal misali, lokacin da aka samu barkewar annobar cutar gubar salmonella (ta zazzabin typhod) shekara shida da ta wuce ta fi addabar kananan yara.
Kasancewar takardar tambayoyi ba ta haifar da wani sakamako mai alfanu ba, sai masu bincike suka sake sabon salo. Sai suka gano cewa mafi yawan marasa lafiyar suna da akwakwun gilashi.
Tashin hankalin shi ne barkewar annobar asalinta ba daga abinci ba ne, amma an ganota a jikin kwado; wadan kwadon Afirka, wanda marasa lafiya suka ajiye a gida don sha'awa.
Da aka ja hankali kamfani da ke kiwata dabbar sai aka gudanar da binciken da ya kawo karshen barkewar annobar.
Wannan lamari ya haifar da kyakkyawan sakamako. Alal misali fda aka samu barkewar annobar gubar salmonella shekara shida da ta wuce sai ta kasance ta fi addabar kananan yara.
Takardun tambayoyi ba su yi wani tasiri mai kyau ba, don haka masu bincike suka sake salo. Daga nan suka gano cewa mafi yawan majiyatan suna da akwakun gilashi (na saka halittun ruwa).
Abin damuwa game da annobar ba a ganota a cikijn abinci ba, amma sai a jikin kwado; nau'in wadan Afirka, wanda marasa lafiyar suka ajiye a gidajensu ddonb sha'awa.
Da aka ja hankalin kamfano nin da ke kiwata irin wannan dabbar sai aka yi binciken da ya kawo karshen annobar.
Dangane da barkewar annobar kwayar cutar E.coli, an gano cewa dabi'un marasa lafiyar ya taimaka wajen bin kadin lamarin.
Jami'in binciken sirri kan barkewar annnoba da aka dora wa alhakin bin kadin lamarin ya fahimci cewa tashin farko mutanen da suka kamu da cutar mfi yawansu mata ne kuma suna yawan aikin kwaba garin fulawa.
Abin damuwar an ga burrbushin kwayar cutar E.coli a jikin ganyayyaki da naman da ba a sarrafa ba, amma shin ko su ne musababbi, ko a ce, fulawar na iya haifarwa?
Rikicin shi ne mutane kan zuba fulawarsu a wani mazubi sannan su yi watsi da jakar, don haka yana da wuya a tantance nau'in aboin da suke amfani da shi.
Duk da haka masu binciken suka yi kokarin gano jakunkuna biyu nau'in Gold Medal na fulawar da majiyatan ke amfani da su a gidjensu a jihohi daban-daban.
An yi su ne a masana'anta guda da ke birnin Kansas da Misssouri, inda kwana guda ne tsakaninsu.
Daga bisani "abin ya haifar da barkewar annobar a garemu," a cewar William, "shi ne akwai yara uku wadanda suka ci abinci a wurare uku daban-daban na gidan sayar da abincin al'adun Mexico," a irin wannan alakar, yayin da iyalai ke jiran abincinsu, ma'aikacin gidan abincin ya kan bai wa yara kwababben curin makwalashen da ba sarrafa ba (ball of tortilla dough) su yi wasa da shi.
"Shin daga ina fulawar da aka cura kwabin tortilla ta fito? in ji Williams. "Hakikanin gaskiya sai aka koma masana'antar birnin Kansas, da ta samar da kayan a lokaci guda."
Ba za ka taba zaton burbushin fulawa da ya watsu a dakin girki zai zama matsala ba.
Daga nan sai hukumomin lafiya suka tuntubi General Mills, kamfanin fulawar gold Medal, inda daga bisani suka janye kanyan daga kasuwa, inda suka shawarci masu masu sayen kayan da su yi watsi da irin wadannan kayayyakin da aka yi a daidai wannan lokacin da ake zargi (cewa sun haifar da annobar).
Daidai lokacin da aka kammala binciken barkewar annoba, an tabbatar da bazuwar kwayar cutar E. coli a fulawar da dimbin majiyatan suka yi amfani d aita, inda mutum 63 suka kamu da rashin lafiya, kodayake an yi sa'a babu wanda yam utu.
Daga nan aka fara tattaunawa kan fulawar, a cewar Williams.
Don haka sai aka yanke cewa a rika dafa fulawa kafin a ci. Kuma kada a dauka cewa burbudin fulawa a dakin girki ba zai iya haifar da cuta ba.
Sai dai kayan amfanin gona da ba a sarrrafa (dafa) ba, a karshe, wadanda aka debo daga gona ko nau'in dabbbobi (wadanda za su iya yada kwayar cutar E.coli).
Da zarar an sarrrafa tsirrai, inda alkama da ta fito daga wurare daban-daban a lokaci guda, ta yadda gubar wata gona na da tasirin yaduwa da yawa.
Barkewar annoba tunatarwa ce kan cewa a daina cin abincin da ba a sarrafa ba( kamar kwababbiyar fulawa ko curin kayan makwalashe da za a soya).
Wannan na nuni da cewa kamfanonin ko masana'antun za su fahimci cewa mutane za su iya kamuwa da rashin lafiya daga sinadarin kwaba fulawa.
Sai aka rika dauka lamarin na tattare da hadari, inda ake lura da guba, sai suka bullo da dabarrun shawo kan lamarin, tun daga kan alkamar da ke tsaye a gona (ba a girbe ba) zuwa ga masana'antar da ake sarrrafata, inda ake ganin yiwuwar ceton rayukanan gaba.
Daukacin wannan aikin rana guda ne, na duba-garin da suka gano gubar da ke gurbata abinci.
Source: BBC Hausa