Masanin dangantakar tattalin arziki da salon mulki (a tsarin siyasa) Benjamin Friedman ya kwatanta al'ummar Turawan Yamma na zamani da keken da ya daidaita da tayoyinsa ke wulwulawa saboda bunkasar tattalin arziki.
Da zarar wulwular tayoyin ta samu tsaiko ko ma ta dakata, turakun da ke kimanta matsayin al'umma a dimokuradiyya da 'yancin walwalar daidaiku da zamantakewar yarda da dabi'un juna da sauransu, to za a yi ta samun kwan-gaba, kwan-baya.
Duniyarmu za ta yi matukar muni, inda za a yi ta fafutikar mamaye 'yan albarkatun kasa tare da kin amincewa da duk wanda ba ya da kusancin danganta da rukuninmu.
Da zarar mun kasa motsa wadannan tayoyi sun ci gaba da juyawa, kawai za a samu rugujewar al'umma dungurungum.
Irin wannan rugujewar ta faru da dama a tsawon tarihin dan Adam, ba tare da ci gaba ba, ko la'akari da tumbatsarta, babu wata kariya da ke bijiro da hadarin da ke rusa al'umma ta zo karshe.
Ba tare da la'akari da kyatatuwar al'amura a halin yanzu ba, yanayin na iya sauyawa.
Fita batun rukunin halittu da suka kare al'amura irin farmakin kananan tairaruwa mai wutsiya (duniyoyin da ke kan falaki) da bazuwar makaman kare dangin nukiliya ko annobar yaduwar cututtuka, tarihi ya nuna mana cewa akwai dimbin al'amura da ke haifar da rushewar al'umma.
Wadanne iri ne, ya ya suke idan akwai su, ko sun fara bijirowa ba kakkautawa? Ba za a ji mamakin cewa al'umma na gudana ko ana tafiyar da ita bisa tsarin dab a zai dore ba, kuma rashin tabbas ne tafarkin da aka dauka, amma abin dubi shi ne ko kawai mun kusa yin nisan da ba ma jin kira?
Duk da cewa yana da wahala a gano hakikanin abin da zai faru nan gaba, lissafi da kimiyya da tarihi na bayar da haske kan ci gaba da kyakkyawar makomar al'ummomin Yammacin Turai.
Safa Motesharrei, masanin kimiyya zayyanar tsare-tsaren al'amura a Jami'ar Maryland ya yi amfani da kwamfuta don samun karin fahimta kan yadda al'amuran kasa ko fadin duniya za su dore ko su wargaje.
A cewar Motesharrei, abin da suka gano shi da abokan aikinsa, wanda aka wallafa a shekarar 2014, akwai muhimman al'amura biyu da ke da tasiri wato: gurbata muhalli da kimanta tattalin arziki mataki-mataki.
Ta fuskar muhalli an fi gano yadda lamarin ke da mummunan tasiri, musamman yadda ake karar da albarkatun kasa, da suka hada da ruwa da kasa da kifaye da dazuka, daukacin al'amuran da ake ganin sauyin yanayi na iya ta'azzara su.
Musifa na aukuwa ne daidai lokacin da shugabanni suka tursasa al'umma ta shiga mawuyacin hali, ta yadda mamaye dimbin dukiya da albarkatun kasa ke haifar da rushewarta.
Kimanta darajar tattalin arziki bisa mataki-mataki na iya haifar da rushewa a kashin kansa, ko kuma ta wani bangaren Montesharrei ya cika da mamakin lamarin shi da abokan aikinsa.
Domin a irin wannan yanayi jagorori kan tursasa al'umma ta shiga mawuyacin hali, ta yadda mamayar da suka yi wa dimbin dukiya da albarkatun kasa za ta haifar da rushewarta, inda za a bar talakawan da suka fi su yawa da kaso dan kadan ko ma su rasa komai kacokam, alhali su ke tallafa musu da aikin kwadago.
Kwatsam sai gungun 'yan kwadago su tarwatse saboda kason dukiyar da aka ware musu ba za ta isa ba, baya ga tarwatsewa saboda rashin aikin kwadago.
Rashin daidaiton adalcin da muke gani a yau a ciki da tsakanin kasashe tuni ya yi nuni da bambance-bambance da ke tsakanin al'umma (talakawa da shigabanninsu).
Haka kuma kimanin rabin al'ummar duniya suna rayuwa ne a kasa da Dalar Amurka uku ko wacce rana ($3).
A irin wadannan nau'ukan yanayi fasalin zayyanar lissafi na nuni da kimar nauyin da yawan al'umma zai iya dauka bisa la'akari da albarkatun da ke tarairayar zamansu a muhallin da suke na tsawon lokaci.
Idan aka jibga musu dimbin nauyin da ya fi karfinsu, to ba makawa al'ummar za ta wargaje. Ba makawa haka makomarsu take.
"Idan muka yi aiki da tunani na hankali don shawo kan irin wadannan matsalolin da suka hada da rashin daidaiton adalci da tumbatsar yawan al'umma, ta yadda ake kwashe dimbin albarkatu da gurbatu muhalli, sai a himmatu kan mai yiwuwa don kauce wa rugujewa don daidaita al'amura su dore ba kakkautawa," a cewar Motesharrei.
"Sai dai ba za mu taba yin jinkiri wajen yanke matsauya kan daukar irin wadannan matakan."
Takaicin shi ne wasu kwararru na jin cewa irin tsauraran matakan da aka dauka sun sha gaban tsarin siyasa da karfin tunaninmu.
"Duniya ba za ta taba mikewa don tunkarar matsalar sauyin yanayi a cikin wannan karnin ba, saboda kawai lamari zai ci dimbin kudi na wucin gadi kafin a warware matsalar sabanbin yadda a ko da yaushe ake kwan gaba, kwan baya," a cewar Jorgen Randers.
Farfesan da ya kai makura a nazarin dabarun tarairayar yanayi a makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta BI Norwegian, kuma marubuci littafin 2052:
Hasashen yanayin duniya nan da shekaru 40. "Matsalar yanayi za ta kara munana saboda mun ki zama mu yi aiki tukuru don cika alkawarin da muka dauka a birnin Paris da sauran wurare.
Duk da cewa a tare muke, wadanda suka fi talauci a duniya su za su tasirin radadin rushewar tashin farko. A gaskiya wasu kasashen sun zama wajen hakar kwal har ta kai ga sun kassara masu dimbin arziki.
Alal, misali Siriya sun yi ta hayayyafa na tsawon lokaci, al'amarin da ya sanya al'ummarsu ta karu. Mummunan farin da aka yi fama da shi cikin shekarun 2000, ta yiwu shi ya haifar da sauyin yanayi tattare da karancin ruwa, ala'amarin da ya kassara harkokin noma.
Wannan mummunar matsala ta jefa dimbin mutane musamman matasa cikin rashin aikin yi da damuwa. Da yawa sun fantsama cikin birane, inda suka mamaye albarkatun kasa da kayan more rayuwa da ke wuraren.
Tashin-tashinar tsakanin al'umma ta dada karuwa, inda aka karke da ruikicin tashin hankali.
Fiye da wannan ma rashin managarcin shugabanci wanda ya hada da jari hujjar jan ragamar kaya su samar wa kansu kimar daraja a kasuwa, al'amarin da ya kawar da tallafi a lokacin farin shi ya share wa kasar kafar afkawa yakin basasa a shekarar 2011, al'amarin da ke kokarin kaita kasa.
Wata alamar da ke nuni da cewa mun shiga da'irar hadari ita ce yawan aukuwar al'amura "kwatsam" sauye-sauyen da ba a zata ba da ke bibiyar duniya.
Dangane da Siriya tamkar na sauran al'ummomi da suka durkushe a daukacin tarihi ba abu daya ya haifar da lamarin ba, akwai dimbin dalilai da suka haifar da matsalar, a cewar Thomas Homer-Dixon, shugaban sashen nazarin tsare-tsaren duniya a Makarantar nazarin harkokin duniya ta Balsille da ke Waterloo a Canada.
Haka kuma marubucin littafi mai taken Jirkicewar al'amura (the Upside Down) Homer-Dixon ya kira daukacin al'amuran da karon-battar yamutsi bisa la'akari da yadda suka taru, sannan suka famtsama kwatsam, inda suka bankara duk wani tsari na daidaita harkokin rayuwa, wanda ke shawo kan matsalolin al'umma.
Baya ga lamarin Siriya, wata alamar da muke kutsawa cikin hadarinta, a cewar Homer Dixon ita ce yawan aukuwar abin da masana ke kira bijirowar rudani da rikice-rikice kwatsam ko aukuwar sauye-sauyen da ba a zata a tsarin tafiyar da harkokin duniya, kamar yadda a shekarar 2008 aka samu matsalar tattalin arziki da fitowar kungiyar ta'addanci ta ISIS da yunkurin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai da zaben Donal Trump.
Source: BBC Hausa