Wata mata ta taimakawa wani tsohon abokinta, inda yanzu ya daina shan miyagun kwayoyi bayan ya kwashe shekara yana gararanba a kan titi.
Al'amarin ya faru ne a farkon watan Oktoba. Wanja Mwaura mai shekara 32 tana kan hanyarta ta zuwa kasuwa a unguwar Lower Kabaete, wadda ba ta da nisa daga birnin Nairobi.
Sai ta ji wani ya kwala mata kira. Da ta waiyawa sai ta ga wani dogon mutum mai kwala-kwalan idanuwa sanye da bakaken tufafu da hula, yana zaune jefan hanya. Sai dai ita ba ta gane shi ba.
Amma da Patrick wanda ake kira Hinga ya gabatar da kansa, sai Wanja ta kidime.
Mutumin da ke gabanta wani tsohon abokinta ne lokacin da take da shekara bakwai a duniya.
"Patrick ko Hinga kamar yadda muke kiran shi, na hadu da shi ne lokacin da nake makarantar firamare a shekarar 1992," in ji Wanja wanda ma'aikaciyar jinya ce daga yankin Kiambu, wanda yake wajen babban birnin Kenya.
"Hinga ya kasance gwani wajen kwallon kafa yayin da muke makaranta. Mun rada masa suna 'Pele'."
Hinga ba ya tare da iyayensa, sai dai yana zaune ne wurin kakarsa a wani dan karamin daki.
Ya daina zuwa makaranta ne saboda yadda ya gaza biyan kudin makaranta.
A karshe kuma ma an tashe su daga dakin da suke zaune.
Amma duk da haka Hinga ya ci jarabawarsa, har sai bayan da kakarsa ta rasu - daga nan ne sai ya daina zuwa makaranta kuma sai rayuwarsa ta fara tabarbarewa.
Hinga ya fara shan miyagun kwayoyi, kodayake da farko ya fara ne da shan wiwi.
Yakan kwashe lokaci mai tsawo yana tone shara don neman abin da tsinta ya sayar.
Hinga da Wanja ba su kara jin duriyar junansu ba.
Sai bayan fiye da shekara 15 ne suka sake haduwa, Hinga yana kwana ne a kan titi fiye shekara 10.
Babu wata alama da za ka ganni a jikinsa wadda za ta nuna cewa yaron nan ne da ake kira Pele.
Ganin yadda Wanja ta fusata, sai Hinga ya ce ya yi mata magana ne kawai don ya gaishe ta.
Ta tambaye shi ko ta saya masa abinci.
Daga nan ne sai ta sayo masa nau'in abincin da ya fi kaunar ci lokacin da yake yaro - wato kashin awazan alade da damamman dankali.
Ta ce daga nan ne sai ya rude, ya kasa magana.
"Na ba shi lambar wayata kuma na shaida masa cewa ya kira ni idan yana bukatar wani abu," in ji Wanja.
Bayan wasu kwanaki, Hinga ya karbi aron waya wanda da ita yake kiran Wanja lokaci zuwa lokaci, musamman ma don ya ji muryarta.
Ya shaida mata cewa a shirye yake ya daina tu'ammali da miyagun kwayoyi.
"Akwai wani abu da ya kamata a yi don taimakon shi," in ji Wanja.
Ta hanyar amfani da shafinta na sada zumunta, Wanja ta bukaci abokanta da su taimaka da kudin da za a taimaka wajen dawo da Hanga cikin al'umma.
"Kai mutum cibiyoyin kintsa masu shaye-shaye tana da tsada sosai kuma ba ni da kudin da zan iya biya ni kaina," in ji ta.
"Mun kafa wani shafi, amma daga farko mun iya samun shilling din Kenya 41,000 (fam 300) ne kawai."
Kodayake ana biyan shillings 100,000 ne a tsawon kwana tara idan aka kai mutum cibiyar Chiromo Lane Medical Center da ke Nairobi.
"Ba mu san inda za mu samo cikin kudin ba."
Amma kuma Wanja ta dauki alkawarin taimaka wa Hinga, don haka sai muka kai shi cibiyar ba tare da sanin abin da zai faru a karshe ba.
Wani mai magana da yawun cibiyar ya ce Hinga wani mutum ne da ya dukufa kan tarbiyyar da aka dora shi a kai a tsawon kwana taran da ya yi a wurinsu.
Cikin 'yan kwanaki Hinga ya fara murmurewa, ya fara jiki kuma natsuwarsa ta dawo.
Daga nan ne sai Wanja ta ce shafin Facebook don ta ba da labarin yadda Hinga ya murmure cikin dan kankanin lokaci.
"A mako guda da ya wuce idan ina magana da Hinga sai na rika sa hannu ina tallabar kansa saboda na tattara hankalinsa wuri guda. A yau za mu iya yin magana yana kallona ina kallonsa," kamar yadda Wanja ta wallafa a shafin Facebook.
Wani dan kasuwa daga birnin Mombasa, Fauz Khalid, ya ga wannan sako a Facebook inda ya ce zai yada sakon don sauran jama'a su gani.
Ya wallafa hotunan a shafinsa na Twitter kuma a yanzu fiye da mutum 50,000 sun yada hotunan ga duniya.
Bayan haka ne kafafen yada labaran Kenya suka fara yada labarin kuma daga nan cibiyar Chiromo Lane Medical Center ta ce ta yafe kudin maganin da ta yi wa Hinga.
Wanja ta ce wannan "abin alheri ne", amma ta ce ta damu sosai ga Hanga don ganin ya murmure gaba daya kuma yanzu ta fara neman masa taimakon kudi, inda zai yi kwana 90 a cibiyar Retreat Rehabilitation, wurin da yake a halin yanzu.
Akwai 'yan Kenya tsakanin 20,000 zuwa 50,000 wanda suke shan tabar ibilis ta Heroin, amma kuma kasar ba ta da cibiyar kintsa masu shan miyagun kwayoyi ko guda.
"Sai dai har yanzu ana kyamar masu shan miyagun kwayoyi a Kenya," in ji Wanja.
Kuma wannan yana iya zama daya daga cikin dalilan da suka sa gwamnati ta ki samar da magunguna kyauta a cibiyoyin kintsa masu shan miyagun kwayoyi.
"Cibiyoyin suna da tsada kuma yawancin mutane ba za su iya kai kansu can ba, ba kawai a Kenya ba amma har sauran sassan nahiyar Afirka. Na dukufa wajen ganin al'umma ta taimake ni don na taimaki abokina," in ji Wanja.
"Wanja wata mutuniyar kirki ce wadda Allah Ya aiko ta. Ba zan iya biyanta ba, ko da zan sadaukar da raina ne. Ta min taimakon da ya fi wanda 'yan uwana za su yi min," kamar yadda Hinga ya shaida wa BBC.
Haka aka rika yayata wannan kalaman da Hanga ya yi a shafukan sada zumunta.
Wani masani kan harkokin hada-hadar kudi, Abraham Wilbourne, wanda yake zaune a Nairobi ya ce "Wanja tana da gida a aljannah!"
Yawancin mutane suna kiranta da sunan "mashujaa," wato ana nufin gwarzuwa a harshen Swahili.
"Mutane suna cewa na sauya rayuwar Hinga, amma shi ma ya sauya tawa rayuwar." in ji Wanja.
"Yanzu na gane cewa karamar tattaunawa za ta iya sauya rayuwar wani."
Source: BBC Hausa